حسان بن ثابت بن المنذر
الإسم
Hassan dan Sabit
اسم الشهرة
Hassan dan Sabit
نبذة مختصرة
Hassan dan Sabit dan Munzir dan Haram mutumin Madina daga Khazraj banajjare, mawakin Ma’aikin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ana mishi alkunya da Abu Walid, ita ce tafi shahara,da Abul Mudarrab da Abul Husam da Abu Abdurrahman, ya inganta cewa annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana sanya wa Hassan minbari a Masallaci ya tsaya akan shi a tsaye, ya yi zambo ga masu yi wa Manzon Allah tsita da amincin Allah su tabbata a gare shi zambo, sai Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: ((Lalle rai mai tsarki yana tare da Hassan muddin, yana bada kariya ga Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agare shi)), Ibnu Sa’ad ya ce: ya rayu a Jahilyyah shekaru sittin, a musulunci ma shekara sittin. Ya rasu yana da shekara dari da ashirin, a shekara ta 54, bayan hijira.