جبير بن مطعم بن عدي بن نوفل
الإسم
Jubair dan Mut’im dan Adi dan Naufal
اسم الشهرة
Jubair Bin Mud'im -Allah ya kara yarda a gareshi-
نبذة مختصرة
Jubair dan Mut’im dan Adiy dan Naufal dan Abdu Manaf Bakuraishe daga Naufal, sahabi ne, ya kasance cikin manyan Kuraishawa, kuma cikin malamai masana dangantaka, ya zo wurin annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- cikin ‘yantattun ribatattun Badar, sai ya ji shi yana karanta Al-Tur a sallar magariba, sai ya ce: Sai hakan ya kasance farkon da imani ya shiga zuciyata, annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya ce: Da Mut’im dan Adiy ya kasance a raye ya yi mini maganar wadannan masu warin da na ba shi su)). Yana nufin ribatattun Badar, Bukhari ne ya ruwaito, Jubair ya musulunta tskanin Hudaibiya da Fath, wasu suka ce a Fath ya musulunta , ya rasu a zamanin Halifancin Mu’awiya shekara ta 59, bayan hijira.