تماضر بنت عمرو بن الحارث بن الشريد
الإسم
Tumadur ‘yar Amr dan Haris dan Sharid
اسم الشهرة
Khansa’u
نبذة مختصرة
Tumadur ‘yar Amr dan Haris dan Sharid mutumin Riyah Basalamiya, an yi Mata lakabi da Khansa’u ta kuma Shahara da lakabin, ita ce mafi shaharar mawakan Larabawa cikin Najad, mafi yawancin shekarunta ta yi su ne a zamanin Jahiliyya, ta kuma shahara begen ‘yan uwanta biyu Sakhar da Mu’awiya, ta riski Musulunci kuma ta Musulunta, ta zo wurin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - tare da mutananta banu Sulaim, tana da ‘ya’ya Maza hudu sun halarci yakin Kadisiyyah shekara ta 16, bayan hijira, kuma ta zaburar da su akan dagewa har aka kashe su bakidayansu ta ce: Nagodewa Allah da ya albarkace ni da shadarsu. Ta rasu a shekara ta 24 bayan hijira.