بلال بن رباح الحبشي
الإسم
Bilal dan Rabah mutumin Habasha
اسم الشهرة
Bilal dan Habasha
نبذة مختصرة
Bilal dan Rabah mutumin Habasha, Ladani, shi ne Bilal dan Rabah dan Hamama, ita ce babar sa, Abubakar Siddik ya saye shi daga wurin mushirikai, lokacin da suka kasance Suna azabtar da shi akan Tauhidi (kadaita Allah) sai ya ‘yanta shi, sai ya lazimci annabi- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya yi masa kiran sallah, ya halarci dukkan yakoki tare da shi, kuma Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya hada ‘yan uwantaka tsakanin shi da Abu Ubaida dan Jarrah, Ammar ya ce: Kowa ya fadi abinda suke so - yana nufin mushirikai- banda Bilal, sannan Bilal ya fiita bayan Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana mai jihadi har lokacin da ya rasu a Sham, shekara ta 20, bayan hijira.