أنس بن مالك بن النضر الأنصاري
الإسم
Anas ɗan Malik ɗan Nadhar mutumin Madina.
اسم الشهرة
Anas ɗna Malik - Allah Ya yarda da shi -.
نبذة مختصرة
Baban Hamza ko baban Sumamah, Anas ɗan Malik ɗan Nadar ɗan Damdam mutumin Madina, daga Najjar da Khazraj al-Basari, babban sahabi ne, an haife shi shekar ta 10, hadimin ma’aikin Allah -tsira da amincin su tabbata a gare shi-, kuma yana daga cikin masu ruwaito hadisai da yawa, kuma ƙarshen sahabin da ya rasu a Basra, haƙiƙa Annabi- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya yi masa addu’a ya ce: «Ya Allah ka yawaita dukiyarsa da ‘ya’yansa ka shigar da shi aljanna» Ya fita tare da Manzan Allah- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- zuwa Badar yana yaro, yana yi masa hidima. Lokacin da Abubakar- Allah Ya yarda da shi- ya zama Halifa sai ya aika masa domin ya tura shi zuwa Bahrain, sai Umar ya je wurin Abubakar, sai Abubakar ta shawarci Umar, sai ya ce ka aika shi yana da wayau, kuma marubuci ne, sai ya aika shi. Ya rasu shekara ta 93.