Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai taɓa yaƙar wasu mutane ba har sai ya kirasu (zuwa ga Addini)
Daga Abdullahi Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - ya ce:
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai taɓa yaƙar wasu mutane ba har sai ya kirasu (zuwa ga Addini).
مَا قَاتَلَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَوْمًا قَطُّ حَتَّى يَدْعُوَهُمْ.
Ibnu Abbas - Allah Ya yarda da su - ya bada labarin cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bai taɓa farawa da yaƙar wasu mutane ba har sai ya kirasu zuwa ga Musulunci a farko, idan ba su amsa kiransa ba sai ya yaƙe su.
An sharɗanta kira zuwa ga Musulunci kafin yaƙi idan Musuluncin bai isa zuwa garesu ba.
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance yana kiransu zuwa Musulunci, idan sun ƙi sai ya bijiro musu da bada da jizya, idan sun ƙi sai ya yaƙesu, kamar yadda ya zo a cikin wasu hadisan daban.
Hikima a cikin yaƙi ita ce shigar mutane cikin Addinin Musulunci, ba wai kwaɗayi a kan bayinsu ko dukiyoyinsu da garuruwansu ba.
Musnad Ahmad (4/ 16) (2105).
Sunan Al-kubra Na Baihaki (9/ 181) (18232).
Kari (1)
تحفة الأحوذي (5/ 130).