Skip to content

Mun kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alhali mu muna samari, sai muka san imani kafin mu koyi alƙur'ani, sannan muka koyi alƙur'ani, sai imaninmu ya ƙaru da shi

Daga Jundub Ibnu Abadullahi - Allah Ya yarda dashi - ya ce:

Mun kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alhali mu muna samari, sai muka san imani kafin mu koyi alƙur'ani, sannan muka koyi alƙur'ani, sai imaninmu ya ƙaru da shi.

كُنَّا مَعَ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ وَنَحْنُ فِتْيَانٌ حَزَاوِرَةٌ، فَتَعَلَّمْنَا الإِيمَانَ قَبْلَ أَنْ نَتَعَلَّمَ القُرْآنَ، ثُمَّ تَعَلَّمْنَا القُرْآنَ، فَازْدَدْنَا بِهِ إِيمَانًا.

Ibnu Majah ne ya ruwaito shi
Ingantacce ne
Bayani

Jundub ibnu Abdullahi - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Mun kasance tare da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - alhali mu muna samari mun kusa balaga, ƙarfafa masu tsananin ƙarfi, sai muka san imani a wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kafin mu koyi Alƙur'ani, sannan muka koyi Alƙur'ani, sai imaninmu ya ƙaru da shi.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

Bayanin cewa imani yana ƙaruwa kuma yana raguwa.

Jeranta abin da ya fi kamata a lokacin tarbiyyar mai tasowa, da kuma kwaɗayi akan cika musu imani.

Alƙur'ani yana ƙara imani, kuma zuciya tana haskaka da shi, kuma ƙirji yana buɗewa da shi.

Manazarta

Sunanu Ibn Majah (1/ 42) (61).

Kari (2)

مشارق الأنوار الوهاجة ومطالع الأسرار البهاجة في شرح سنن الإمام ابن ماجه (2/ 255).

مرشد ذوي الحجا والحاجة إلى سنن ابن ماجه والقول المكتفى على سنن المصطفى (1/ 227).