Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya cewa Abubakar da Umar: "Waɗannan biyun sune shugabannin dattijan 'yan aljanna daga na farko dana ƙarshe sai dai Annabwa da Manzanni
Daga Anas - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya cewa Abubakar da Umar: "Waɗannan biyun sune shugabannin dattijan 'yan aljanna daga na farko dana ƙarshe sai dai Annabwa da Manzanni".
قال رسول الله صلى الله عليه وسلم لأبي بكر وعمر: «هذان سَيِّدا كُهُول أهل الجنة من الأوَّلِين والآخِرين إلا النبيِّين والمرسلين».
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bada labarin cewa Abubakar Siddiƙ da Umar Faruƙ - Allah Ya yarda da su - sune mafifitan mutane bayan Annabawa, kuma mafifitan waɗanda suka shiga aljanna bayan Annabwa da Manzanni.
Abubakar da Umar - Allah Ya yarda da su - sune mafifitan mutane bayan Annabawa da Manzanni.
A aljanna babu tsoho, kai, wanda zai shigeta ɗan shekara talatin da uku ne, abin nufi cewa sune shugabannin wanda ya mutu yana dattijo a duniya, ko kuma hakan izina ne na abinda suke akansa a duniya a lokacin wannan hadisin.
Sunan Tirmizi (6/ 45) (3664).
Kari (2)
تحفة الأحوذي بشرح جامع الترمذي.
لمحمد المباركفوري (10/ 103).