Skip to content

Duk abinda mai yawansa yake sa maye to kaɗan ɗinsa haramun ne

Daga Jabir ɗan Abbdullahi - Allah Ya ƙara yarda a gare su - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:

"Duk abinda mai yawansa yake sa maye to kaɗan ɗinsa haramun ne".

«مَا أَسْكَرَ كَثِيرُهُ فَقَلِيلُهُ حَرَامٌ».

Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi
Hasan ne
Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa dukkan abin sha ko abin ci da yake kawar da hankali lokacin da aka ci ko aka sha mai yawa daga gare shi, to cin kaɗan daga gare shi abin haramtawa ne koda bai tafiyar da hankali ba.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

Kiyayewar shari'a akan hankulan mutane.

Ingancin lura da toshe kafa, hakan ta hanyar kulle dukkan abinda yake kaiwa zuwa waɗannan munanan abubuwan.

Haramta kaɗan na abinda yake sa maye; domin shi tsani ne ga maye.

idan kaɗan ɗinsa ko mai yawansa baisa maye ba, to shi ba haramun ba ne.

Manazarta

Sunan Abi Dawud (5/ 523) (3681).

Sunan Tirmizi (3/ 442) (1865).

Sunanu Ibn Majah (4/ 475) (3393).

Musnad Ahmad (23/ 51) (14703).

Kari (3)

فتح ذي الجلال والإكرام بشرح بلوغ المرام (5/ 418).

شرح سنن أبي داود للعباد (417/ 9).

النهاية في غريب الحديث والأثر (437).