Skip to content

Na haɗu da (Annabi) Ibrahim a daren da aka yi Isra'i dani sai ya ce: Ya Muhammad, ka yi wa al'ummarka sallama daga gareni, kuma ka basu labarin cewa aljanna mai daɗin turɓaya ce mai daɗin ruwa ce

Daga Ibnu Mas'ud - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:

"Na haɗu da (Annabi) Ibrahim a daren da aka yi Isra'i dani sai ya ce: Ya Muhammad, ka yi wa al'ummarka sallama daga gareni, kuma ka basu labarin cewa aljanna mai daɗin turɓaya ce mai daɗin ruwa ce, kuma ita faƙo ce kuma dashenta (shi ne): Subhanallah, (tsarki ya tabbata ga Allah), Alhamdulillah (godiya ta tabbata ga Allah), Lailaha Illallahu, (babu abin bautawa da gaskiya sai Allah), Allahu Akbar (Allah ne Mafi girma)".

«لَقِيتُ إِبْرَاهِيمَ لَيْلَةَ أُسْرِيَ بِي فَقَالَ: يَا مُحَمَّدُ، أَقْرِئْ أُمَّتَكَ مِنِّي السَّلاَمَ، وَأَخْبِرْهُمْ أَنَّ الجَنَّةَ طَيِّبَةُ التُّرْبَةِ عَذْبَةُ الْمَاءِ، وَأَنَّهَا قِيعَانٌ، وَأَنَّ غِرَاسَهَا سُبْحَانَ اللهِ وَالحَمْدُ لِلَّهِ وَلاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ وَاللَّهُ أَكْبَرُ».

Tirmizi ne ya ruwaito shi
Hasan ne a baki dayan Riwayoyin sa
Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa ya haɗu da (Annabi) Ibrahim badaɗayi - aminci ya tabbata agare shi - a daren Isra'i da Mi'iraji, sai ya ce masa Ya Muhammad; Ka isarwa da al'ummarka sallama daga gareni, kuma ka sanar dasu cewa aljanna mai daɗin turɓaya ce, mai daɗin ruwa ce babu zartsi a acikinsa, kuma aljanna mai faɗi ce madaidaiciya ce babu itatuwa a cikinta, dashenta (shi ne) kalmomi masu tsarki, sune wanzajju na gari: Tsarki ya tabbata ga Allah, godiya ta tabbata ga Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Allah ne Mafi girma, duk lokacin da musulmi ya faɗesu kuma ya maimaita su za'a yi masa dashe a cikin aljanna.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

Kwaɗaitarwa akan dawwama akan zikiri dan yawaita dashen aljanna.

Falalar al'ummar musulmi; inda (Annabi) Ibrahim - tsira da aminci su tabbata agare shi - ya isar mata da sallama.

Kwaɗaitarwa (Annabi) Ibrahim - aminci ya tabbata agare shi - ga al'ummar (Annabi) Muhammad - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - cikin yawaitawa daga ambatan Allah - Maɗaukakin sarki -.

Malam al-Ɗaibi ya ce: Aljanna ...?, sannan Allah - Maɗaukakin sarki - Ya samar mata da bishiyoyi da katangu da falalarsa gwargwdan ayyukan masu aiki; kowane mai aiki akwai abinda ya keɓanta da shi saboda aikinsa, sannan cewa Shi - Allah Maɗaukakin sarki - yayin da Ya sawwaƙa masa dan abinda Ya halicce shi saboda shi na aiki dan ya samu lada da hakan sai Ya sanya shi kamar mai dasa waɗancan bishiyoyin.

Manazarta

Sunan Tirmizi (5/ 455) (3462).

Kari (11)

بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين لسليم الهلالي (2/ 512).

الكاشف عن حقائق السنن (شرح المشكاة).

للطيبي (6/ 1831).

كنوز رياض الصالحين.

لمجموعة من الباحثين (17/ 186).

مشكاة المصابيح.

للتبريزي (2/ 716).

مرعاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح.

للمباركفوري (7/ 476).

نزهة المتقين شرح رياض الصالحين.

لمجموعة من الباحثين (2/ 985).