Kowanne abu da kaddara ne, har gajiya da dabara, ko kuma wayo da gajiya
Daga Dawus cewa shi ya ce: Na riski wasu mutane daga sahabban Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - suna cewa kowane abu (yana kasancewa) da kaddara ne, ya ce: Na ji Abdullahi Ibnu Umar - Allah Ya yarda da su, yana cewa: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce:
"Kowanne abu da kaddara ne, har gajiya da dabara, ko kuma wayo da gajiya ".
«كُلُّ شَيْءٍ بِقَدَرٍ، حَتَّى الْعَجْزِ وَالْكَيْسِ، أَوِ الْكَيْسِ وَالْعَجْزِ».
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa kowanne abu da kaddara ne; Har kasawa: ita ce: Barin abinda yake wajibi ne aikata shi, da cewa zai yi ta jinkirta shi daga lokacinsa, da al'amuran duniya da lahira. Har dabara ita ce: Nishadi da kwarewa da al'amuran duniya da lahira. Kuma cewa Allah - Mai girma da daukaka - hakika Ya kaddara gajiyawa da wayo da kowane abu, ba zai afku a kasantacce ba sai hakika sanin Allah Ya rigaya da shi da mashi'arSa.
...:
Bayanin kudircewar sahabbai - Allah Ya yarda da su - a kaddara.
Kowanne abu yana faruwa ne da kaddarawar Allah har gajiyawa da kuma nishadi.
Ya tabbata kuma sahabbai - Allah Ya yarda da su, sun tsoratar - a cikin riwayar hadisan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
Yin imani da kaddara dukkaninsa alherinSa da kuma sharrinSa.
Sahih Muslim (4/ 2045) (2655).
Kari (3)
إكمال المعلم (8/143).
شرح النووي على مسلم (16/205).
الفتح الرباني لترتيب مسند الإمام أحمد بن حنبل الشيباني (1/ 122).