Skip to content
Jerin Surori /

التَّحرِيم

التَّحرِيم is chapter 66 of the Quran and has 12 verses. This page presents it in full in the Uthmani script, with a verse-by-verse translation of its meaning.

12 Ayoyi Lambar Sura 66
Je zuwa aya
Hausa · Gummi
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّبِيُّ لِمَ تُحَرِّمُ مَآ أَحَلَّ ٱللَّهُ لَكَۖ تَبۡتَغِي مَرۡضَاتَ أَزۡوَٰجِكَۚ وَٱللَّهُ غَفُورٞ رَّحِيمٞ

Yã kai Annabi! Don me kake haramta abin da Allah Ya halatta maka, kanã nẽman yardar mãtanka, alhãli kuwa Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.

Explanation & meanings · 1
  1. A cikin littãfin Buhãri an ruwaito daga A'isha, mãtar Annabi, cewa Annabi, tsĩra da amincin Allah su tabbata a gareshi, yakan yi jinkiri a wajen Zainab bint Jahsh dõmin ya shã zuma a wurinta. Ta ce: "Sai na shirya, nĩ da Hafsah: Duk wadda Manzon Allah ya shiga gurinta daga garemu, ta ce masa, 'Ina jin wãrin tsimi daga gareka! Kã ci tsimi! To, sai Annabi ya shiga ga ɗayansu, ta ce masa: "Kã ci tsimi." Ya ce: "A'isha! Nã shã zuma dai a wurin Zainab bint Jahsh, kuma ba zan kõma gareshi ba." Asalin abin, Annabi tsira da amincin Allah ya tabbata a gareshi,yã kasance yanã zagayãwa a gidãjen mãtansa a bãyan sallar la'asar dõmin ya gaishe su. To, sai ya sh ga ga Hafsah bãyan ya shiga ga Zainab, ta gaya masa haka. Kuma ya gaya mata nĩsantarsa ga zuma, kuma ya gaya mata lãbãrin cewa Abubakar da Umar, Allah Ya yarda da su, za su zama halĩfai a bãyansa. To, sai ta faɗi waɗannan lãbãru ga maƙwabciyarta A'isha. Wannan Ƙissa tana koyar da sauƙin halin Annabi a game da iyãlansa, da girmamawarsa a gare su.

قَدۡ فَرَضَ ٱللَّهُ لَكُمۡ تَحِلَّةَ أَيۡمَٰنِكُمۡۚ وَٱللَّهُ مَوۡلَىٰكُمۡۖ وَهُوَ ٱلۡعَلِيمُ ٱلۡحَكِيمُ

Haƙĩƙa Allah ya faralta muku warware rantsuwõyinku, kuma Allah ne Mataimakinku kuma shĩ ne Masani, Mai hikima.

Explanation & meanings · 1
  1. An rubũta yadda ake warware rantsuwa da kaffãra wadda aka ambata a cikin sũra ta 5, ãyã ta 89. Anã kaffãrar rantsuwa da ciyar da miskĩnai gõma daga matsakaicin abinci, mũdu biyu ga kõwane, kõ tufãtar da su tufar da za ta ishe su salla, idan bai sãmu ba, ya yi azumin kwãna uku.

وَإِذۡ أَسَرَّ ٱلنَّبِيُّ إِلَىٰ بَعۡضِ أَزۡوَٰجِهِۦ حَدِيثٗا فَلَمَّا نَبَّأَتۡ بِهِۦ وَأَظۡهَرَهُ ٱللَّهُ عَلَيۡهِ عَرَّفَ بَعۡضَهُۥ وَأَعۡرَضَ عَنۢ بَعۡضٖۖ فَلَمَّا نَبَّأَهَا بِهِۦ قَالَتۡ مَنۡ أَنۢبَأَكَ هَٰذَاۖ قَالَ نَبَّأَنِيَ ٱلۡعَلِيمُ ٱلۡخَبِيرُ

Kuma a sã'ilin da Annabi ya asirta wani lãbãri zuwa ga sãshen mãtansa, to, a lõkacin da ta bã da lãbari da shi. Kuma Allah Ya bayyana shi a gare shi, ya sanar da sãshensa kuma ya kau da kai daga wani sãshe. To, a lõkacin da ya bã ta lãbãri da shi, ta ce: "Wãne ne ya gaya maka wannan?" Ya ce: "Masani, Mai labartãwa, Ya gaya mini."

إِن تَتُوبَآ إِلَى ٱللَّهِ فَقَدۡ صَغَتۡ قُلُوبُكُمَاۖ وَإِن تَظَٰهَرَا عَلَيۡهِ فَإِنَّ ٱللَّهَ هُوَ مَوۡلَىٰهُ وَجِبۡرِيلُ وَصَٰلِحُ ٱلۡمُؤۡمِنِينَۖ وَٱلۡمَلَٰٓئِكَةُ بَعۡدَ ذَٰلِكَ ظَهِيرٌ

Idan kũ biyu kuka tũba zuwa ga Allah, to, haƙĩƙa zukãtanku sun karkata. Kuma idan kun taimaki jũna a kansa to, lalle Allah Shĩ ne Mataimakinsa, da Jibrĩlu da sãlihan mũminai. Kuma malã'iku a bãyan wancan, mataimaka ne.

عَسَىٰ رَبُّهُۥٓ إِن طَلَّقَكُنَّ أَن يُبۡدِلَهُۥٓ أَزۡوَٰجًا خَيۡرٗا مِّنكُنَّ مُسۡلِمَٰتٖ مُّؤۡمِنَٰتٖ قَٰنِتَٰتٖ تَٰٓئِبَٰتٍ عَٰبِدَٰتٖ سَٰٓئِحَٰتٖ ثَيِّبَٰتٖ وَأَبۡكَارٗا

Mai yiwuwa ne Ubangijinsa, idan ya sake ku, Ya musanya masa waɗansu mãtan aure mafiya alhẽri daga gare ku, Musulmai mũminai mãsu tawãli'u, mãsu tũba, mãsu ibãda, mãsu, azumi, zawarõri da 'yammãta.