66 : 12
وَمَرۡيَمَ ٱبۡنَتَ عِمۡرَٰنَ ٱلَّتِيٓ أَحۡصَنَتۡ فَرۡجَهَا فَنَفَخۡنَا فِيهِ مِن رُّوحِنَا وَصَدَّقَتۡ بِكَلِمَٰتِ رَبِّهَا وَكُتُبِهِۦ وَكَانَتۡ مِنَ ٱلۡقَٰنِتِينَ
Da Maryama ɗiyar Imrãna wadda ta tsare farjinta, sai Muka hũra a cikinsa daga rũhinMu. Kuma ta gaskata game da ãyõyin Ubangijinta da Littattafan Sa alhãli kuwa ta kasance daga mãsu tawãli'u.
Explanation & meanings · 1
- Wannan yanã nũna cewa rashin aure ga mãtar da ke iya tsare farjinta daga alfãsha kuma ta tsare addininta da taƙawa, bã zai cũce ta ba ga sãmun rahamar Allah a dũniya da lãhira.