Skip to content
Jerin Surori /

الشُّورى

الشُّورى is chapter 42 of the Quran and has 53 verses. This page presents it in full in the Uthmani script, with a verse-by-verse translation of its meaning.

53 Ayoyi Lambar Sura 42
Je zuwa aya
Hausa · Gummi
بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

كَذَٰلِكَ يُوحِيٓ إِلَيۡكَ وَإِلَى ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِكَ ٱللَّهُ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ

Kamar wancãn (asĩrin) Allah, Mabuwayi, Mai hikima, ke yin wahayi zuwa gare ka da zuwa ga waɗanda ke gabãninka.

Explanation & meanings · 1
  1. Asirin haɗa jama'a bã zã su rarrabu ba. Watau su riƙi Allah Shi kaɗai ne Ubangiji Mai yin umurni ko hani, kuma su riƙi cewa Muhammadu, tsĩra da aminci su tabbata a gareshi, shĩ ne cikamakin Annabãwa, bãyansa bã a bai wa kõwa kõme fãce fahimta ga abin da ya zo da shi.

لَهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۖ وَهُوَ ٱلۡعَلِيُّ ٱلۡعَظِيمُ

(Allah) Shi ne da abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa, kuma Shi ne Maɗaukaki, Mai girma.

تَكَادُ ٱلسَّمَٰوَٰتُ يَتَفَطَّرۡنَ مِن فَوۡقِهِنَّۚ وَٱلۡمَلَٰٓئِكَةُ يُسَبِّحُونَ بِحَمۡدِ رَبِّهِمۡ وَيَسۡتَغۡفِرُونَ لِمَن فِي ٱلۡأَرۡضِۗ أَلَآ إِنَّ ٱللَّهَ هُوَ ٱلۡغَفُورُ ٱلرَّحِيمُ

Sammai nã kusan su tsãge daga bisansu, kuma malã'iku nã yin tasĩhi game da gõdẽ wa Ubangijinsu kuma sunã istigfãri dõmin wanda ke cikin ƙasa. To, lalle Allah Shĩ ne Mai gãfara, Mai jin ƙai.