Skip to content

Azimi a halin tafiya bai zama daga aikin alheri ba

Daga Jabir ɗan Abdullah -Allah Ya yarda da su -, ya ce:

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance a wata tafiya, sai ya ga cunkoso da wani mutum an yi masa inuwa, sai ya ce: «Menene wannan», sai suka ce: Mai azimi ne, sai ya ce: «Azimi a halin tafiya bai zama daga aikin alheri ba». A cikin wani lafazin na Muslim: «Na horeku da rangwamin da Allah Ya yi muku».

كَانَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فِي سَفَرٍ، فَرَأَى زِحَامًا وَرَجُلًا قَدْ ظُلِّلَ عَلَيْهِ، فَقَالَ: «مَا هَذَا؟»، فَقَالُوا: صَائِمٌ، فَقَالَ: «لَيْسَ مِنَ البِرِّ الصَّوْمُ فِي السَّفَرِ»، وَفِي لَفْظٍ لِمُسلِمٍ: «عَلَيْكُمْ بِرُخْصَةِ اللهِ الَّذِي رَخَّصَ لَكُمْ».

Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
Bayani

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance a cikin wata tafiya, sai ya ga wani mutum mutane sun haɗu a kansa alhali an yi masa inuwa saboda zafin rana da tsananin ƙishirwa, sai ya ce: Me ya same shi ? sai suka ce: Mai azimi ne, sai ya ce: Azimi a halin tafiya bai zama daga cikin ayyukan alheri ba, na horeku da rangwamin da Allah Yayi muku.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

Bayanin sauƙin shari'ar Musulunci.

Halaccin yin Azumi a halin tafiya, da kuma halaccin riƙo da rangwami da barin yin azimin.

An hana yin azumi a halin tafiya idan azumin yana yi masa wahala, muddin dai bai kai iyakar mutuwa ba sai (azimin) ya haramta.

Nawawi ya ce: Ba aikin alheri ba ne ku yi azimi a halin tafiya: ma'anarsa: Idan azumin yana yi muku wahala, kuma kuka ji tsoron cuta, siyaƙin hadisin yana hukunta wannan tawilin.

Kulawar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ga sahabbansa da yadda yake tambayar halayensu.

Manazarta

Sahih Al-Bukhari (3/ 34) (1946).

Sahih Muslim (2/ 786) (1115).

Kari (4)

تيسير العلام.

للبسام (ص327).

تنبيه الأفهام شرح عمدة الإحكام.

لابن عثيمين (3/ 433).