Skip to content

Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani daga yin tsarki da toroson dabbobi ko ƙashi

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce:

Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi hani daga yin tsarki da toroson dabbobi ko ƙashi, kuma ya ce: «‌Lallai su basa tsarkakewa».

إِنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ نَهَى أَنْ يُسْتَنْجَى بِرَوْثٍ أَوْ عَظْمٍ، وَقَالَ: «إِنَّهُمَا لَا تُطَهِّرَانِ».

Dar Al-Kutni ne Ya Rawaito shi
Ingantacce ne
Bayani

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya hana wanda ya biya buƙatarsa na fitsari ne ko bahaya ya yi tsarkin hoge da ƙashin dabbobi ko torosonsa da busassun torosonsa; kuma ya ce: Lallai su basa kawar da najasa, kuma ba'a tsarkaka daga garesu.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

Bayanin wasu daga cikin ladubban bayan gida da kuma tsarki.

Hani daga tsarkin hoge da toroson dabbobi; domin cewa shi: Kodai ya zama najasa, ko kuma domin cewa shi abincin dabbobin aljanu ne.

Hani akan yin tsarkin hoge da ƙashi; domin cewa shi kodai najasa ne, ko kuma domin abincin aljanu ne su da kansu.

Manazarta

Sunan Al-DarAl-Kutni (1/ 88) (152).

Kari (6)

توضيح الأحكام مِن بلوغ المرام.

لعبد الله البسام (1/ 355).

سبل السلام.

للصنعاني (1/ 118).

مرقاة المفاتيح شرح مشكاة المصابيح.

لعلي القاري (1/ 374).