Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana ambaton Allah a kodayaushe
Daga Nana A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce:
Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana ambaton Allah a kodayaushe.
كَانَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَذْكُرُ اللهَ عَلَى كُلِّ أَحْيَانِهِ.
Nana A'isha uwar Muminai Allah Ya yarda da ita, tana ba da bayanin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana tsananin kwaɗayi a kan yin ambaton Allah maɗaukaki, kuma ya kasance yana ambaton Allah a kowanne lokaci da kowanne yanayi.
...:
Ba a sharɗanta tsarkin ƙaramin hadasi ko babba a ambaton Allah ba.
Dawwamar Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a ambaton Allah maɗaukaki.
Kwaɗaitarwa a kan yawaita ambaton Allah maɗaukaki a kowanne lokaci domin koyi da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, sai a yanayin da aka hana ambaton Allah kamar lokacin biyan buƙata.
Sahih Muslim (1/ 282) (373).
Sahih Al-Bukhari (1/ 68).
(1/ 129).
Kari (6)
توضيح الأحكام مِن بلوغ المرام.
للبسام (1/ 315).
فتح ذي الجلال والإكرام شرح بلوغ المرام.
لابن عثيمين (1/ 273).
مجموع فتاوى ومقالات.
لابن باز (26/ 17).