Skip to content

Yana daga cikin sunnah idan mai kiran sallah a kiran sallar Asuba ya ce: Hayya alal falah (Ku yi gaggawa zuwa tsira), to ya ce: Assalatu khairun minan naum (Sallah ta fi bacci alheri)

Daga Anas - Allah Ya yarda da shi ya ce:

Yana daga cikin sunnah idan mai kiran sallah a kiran sallar Asuba ya ce: Hayya alal falah (Ku yi gaggawa zuwa tsira), to ya ce: Assalatu khairun minan naum (Sallah ta fi bacci alheri).

مِنَ السُّنَّةِ إِذَا قَالَ الْمُؤَذِّنُ فِي أَذَانِ الْفَجْرِ حَيَّ عَلَى الْفَلَاحِ، قَالَ: الصَّلَاةُ خَيْرٌ مِنَ النَّوْمِ.

Ibnu Khuzaimah da Dar Al-Kutni da Baihaki ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
Bayani

Anas Ibnu Malik - Allah Ya yarda da shi - ya bada labari, cewa daga abinda Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya tabbatar da shi a cikin sunnarsa, shi ne mai kiran sallah ya ce a cikin kiran sallar Asuba kadai, bayan faɗinsa: (Hayya alal falah (ku yi gaggawa zuwa tsira)), ya ce: (Assalatu khairun minan naum (sallah tafi bacci alheri)).

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

Faɗinsa: (Yana daga sunnah): Yana nufin sunnar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, to shi yana da hukuncin Raf'u, wato wanda aka danganta shi zuwa ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.

An so mai kiran sallah a cikin kiran sallar Asuba ya ce bayan ya faɗi: Hayya alal falah (ku yi gaggawa zuwa tsira): Assalatu khairun minan naum (Sallah ta fi bacci alheri), sau biyu; domin sallar Asuba a lokacin da mutane suke bacci ne a cikinsa, zasu tashi daga bacci zuwa sallah, sai aka keɓanci sallar Asuba da hakan banda sauran sallolin.

Manazarta

Sahih Ibnu khuzaimah (1/ 233) (386).

Sunan Al-DarAl-Kutni (1/ 454) (944).

Sunan Al-kubra Na Baihaki (1/ 623) (1984).

Kari (6)

توضيح الأحكام مِن بلوغ المرام.

لعبد الله البسام (1/ 510).

منحة العلام في شرح بلوغ المرام.

لعبد الله الفوزان (2/ 239).

فتاوى اللجنة الدائمة.

اللجنة الدائمة للبحوث العلمية والإفتاء (6/ 62).