Skip to content
Al'ahzab /

Aya 56

33 : 56

Aya 56 of Al'ahzab (33 : 56). This page carries the verse in the Uthmani script with a translation of its meaning, at a stable URL that can be cited on its own.

Al'ahzab Ayoyi 73
Sura · Al'ahzab
Hausa · Gummi
33 : 56

إِنَّ ٱللَّهَ وَمَلَٰٓئِكَتَهُۥ يُصَلُّونَ عَلَى ٱلنَّبِيِّۚ يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ صَلُّواْ عَلَيۡهِ وَسَلِّمُواْ تَسۡلِيمًا

Lalle, Allah da malã'ikun Sa sunã salati ga Annabi. Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku yi salãti a gare shi, kuma ku yi sallama dõmin amintarwa a gare shi.

Explanation & meanings · 1
  1. Salãtin Allah ga Annabi, shĩ ne ɗaukaka darajarsa a kõyaushe. Salãtin malã'iku, shĩne istigfãri da addu'a a gare shi. Salãtin mutãne, shĩ ne ibãda da istigfãri da addu'a a gare shi da tawassuli da shi dõmin neman Allah Ya karɓi ibãdarsu. Salãti sau ɗaya wãjibi ne a kan kõwane Musulmi a tsawon rayuwarsa, sa'an nan kuma sunna ce a cikin kõwace salla. Kuma mustahabbi ne a cikin kõwane mazauni da wurin ambatonsa.