11 : 114
وَأَقِمِ ٱلصَّلَوٰةَ طَرَفَيِ ٱلنَّهَارِ وَزُلَفٗا مِّنَ ٱلَّيۡلِۚ إِنَّ ٱلۡحَسَنَٰتِ يُذۡهِبۡنَ ٱلسَّيِّـَٔاتِۚ ذَٰلِكَ ذِكۡرَىٰ لِلذَّٰكِرِينَ
Kuma ka tsai da salla a gẽfe guda biyu na yini da wani yanki daga dare. Lalle ne ayyukan ƙwarai sunã kõre mũnãnan ayyuka. Wancan ne tunãtarwa ga mãsu tunãwa.
Explanation & meanings · 1
- Tsayar da sallõli farillai tãre da Lĩman a cikin masallatai shĩ ne zikiri ga mai son zikirin gaskiya. Ayyukan ƙwarai sunã shãfe miyãgu.