Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

5 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
"Mai kai kawo ga wacce mijinta ya rasu ko miskini kamar mai yaki ne a tafarkin Allah, ko mai tsayuwar dare kuma mai azumi da rana".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Ayyuka shida ne, mutane kuma hudu ne, akwai tabbatattu biyu. Da tamka da tamka, da kyakkyawa da tamkarta goma, da kyakkyawa da dari bakwai. Amma masu tabbatattu biyu: Wanda ya mutu ba ya taranya wani abu da Allah zai shiga Aljanna. Wanda ya mutu yana taranya wani abu da Allah zai shiga wuta. Amma tamka da tamka: Wanda ya himmantu da kyakkyawa har ya jiyar da zuciyarsa ita, kuma Allah Ya santa daga gareshi za'a rubuta masa kyakkyawa, wanda ya aikata mummuna, za'a rubuta mummuna akansa. Wanda ya aikata kyakkyawa da tamkarta goma, wanda ya ciyar da wani abu a tafarkin Allah to kyakkyawa da dari bakwai. Amma mutane akwai wanda aka yalwatawa a duniya aka kuntata masa a lahira, da kuma wanda aka kuntatawa a duniya kuma aka yalwata masa a lahira, da wanda aka kuntatawa a duniya da lahira, da wanda aka yalwatawa a duniya da lahira".
Hasan ne Ahmad ne ya rawaito shi
"Mafificin dinaren (kudi) da mutum zai ciyar da shi: Dinarin da ya ciyar da shi ga iyalansa, da dinaren da mutum yake ciyar da shi ga dabbarsa a tafarkin Allah, da dinaren da yake ciyar da shi ga abokansa a tafarkin Allah" Abu Kilaba ya ce: "Sai ya fara da iyali, sannan Abu Kilaba ya ce: Kuma wanne mutum ne mafi girman lada kamar mutumin da yake ciyar da iyali ƙanana don ya rufa musu asiri ko Allah Ya anfanar da su da shi, kuma ya wadata su".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
"Ba za ku shiga aljanna ba har sai kun yi imani, Ba za ku yi imani ba har sai kun so junanku, , shin ba na shiryar daku akan abinda idan kun aikata shi za ku so junanku ba? ku yada sallama a tsakaninku".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
"Idan bawa musulmi ya yi alwala - ko kuma mumini - sai ya wanke fuskar sa, to kowane kuskuren da ya yi kallo da shi da idanun sa zai fice daga fuskar sa tare da ruwa - ko kuma tare da ƙarshen ɗigon ruwa - idan ya wanke hannayen sa, kowane kuskure zai fita daga hannayen sa waɗanda hannayen sa suka damƙa tare da ruwa - ko tare da ƙarshen ɗigon ruwa -, idan ya wanke ƙafafuwan sa kowane kuskuren da ƙafafuwan sa suka tafi gare shi zasu fita tare da ruwa - ko tare da ƙarshen ɗigon ruwa - har sai ya fita tsarkakakke daga zunubai".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi