Skip to content

Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance ya fi kowa kyawawan ɗabi’u

Daga Anas Dan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce:

Ma’aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance ya fi kowa kyawawan ɗabi’u.

كَانَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَحْسَنَ النَّاسِ خُلُقًا.

Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
Bayani

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance ya fi kowa cikar kyawawan ɗabi’u, yana da wannan rigayar a dukkanin kyawawan ɗabi’u, kamar kyakkyawar magana, bayar da kyauta, sakin fuska, rashin cutarwa, juriyarsa ga mutane.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

Cikar ɗabi’un Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, shi ne babban abin koyi a kyawawan ɗabi’u.

Kwaɗaitarwa a kan koyi da Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a kyawawan ɗabi’u.

Manazarta

Sahih Al-Bukhari (8/ 45) (6203).

Sahih Muslim (4/ 1805) (2310).

Kari (8)

بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين.

لسليم الهلالي (1/ 670).

نزهة المتقين شرح رياض الصالحين.

لمصطفى الخِن وغيره (1/ 524).

كنوز رياض الصالحين.

لمجموعة من الباحثين (9/ 57).

شرح رياض الصالحين.

لابن عثيمين (3/ 556).