Skip to content

Wanda yake da mata biyu sai ya karkata zuwa ɗayansu, zai zo ranar alƙiyama alhali ɓarin jikinsa a karkace

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:

"Wanda yake da mata biyu sai ya karkata zuwa ɗayansu, zai zo ranar alƙiyama alhali ɓarin jikinsa a karkace".

«مَنْ كَانَتْ لَهُ امْرَأَتَانِ فَمَالَ إِلَى إِحْدَاهُمَا، جَاءَ يَوْمَ الْقِيَامَةِ وَشِقُّهُ مَائِلٌ».

Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i da Ibn Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi
Ingantacce ne
Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana bada labarin cewa wanda yake da sama da mace (ɗaya), bai yi adalci tsakanin matansa gwargwadon iko ba na daidaitawa tsakaninsu a ciyarwa da wurin zama da abin sawa da wurin kwana, cewa uƙubarsa a ranar alƙiyama ta kasance ne rabin jikinsa a karkace, kuma karkacewarsa uƙuba ce gare shi akan zalincinsa, kamar yadda ya karkata a cikin mu'amalarsa.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

Wajabcin raban kwana akan namiji tsakanin matansa biyu ko matansa da yawa, kuma karkata zuwa ga ɗayansu ya bar sauran yana haramta, a abinda yake da iko akansa na ciyarwa, da wurin zama, da kyakkyawar tarba, da makamancin hakan.

Daidaito a rabon kwana da makamancin haka, a abinda mutum yake iya mallakarsa, amma a abinda ba ya iya mallakinsa kamar soyayya da karkata ta zuciya to cewa shi ba ya shiga cikin hadisin, kuma shi ne abin nufi a cikin faɗinSa - Allah Maɗaukakin sarki -: {Ba zaku iya adalci a tsakanin mata ba koda kun yi kwaɗayi} [al-Nisa'i: 129].

Sakayya tana kasancewa ne daga jinsin aiki, cewa mutum a lokacin da ya karkata a duniya daga wata mace zuwa wata, zai zo a ranar alƙiyama ɗaya daga tsagin jikinsa ya karkace daga ɗayan.

Girmama haƙƙoƙin bayi, kuma cewa ba'a kau da kai a kansu; domin cewa su ababen ginawa ne akan ƙwauro da sakayya.

An so taƙaituwa akan mace ɗaya idan namiji ya ji tsoron kada ya yi adalci tsakanin matansa; dan kada ya faɗa a cikin gazawa a cikin Addini; Allah Maɗaukakin sarki Ya ce: {Idan kuka ji tsoron ba zaku yi adalci ba to (ku auri mace) ɗaya} [al-Nisa'i: 3].

Manazarta

Sunan Abi Dawud (3/ 469) (2133).

Sunanu Nasa'i (7/ 63) (3942).

Sunan Tirmizi (2/ 434) (1141).

Sunanu Ibn Majah (3/ 143) (1969).

Musnad Ahmad (13/ 320) (7936).

Kari (9)

توضيح الأحكام مِن بلوغ المرام.

لعبد الله البسام (5/ 449).

فتح ذي الجلال والإكرام شرح بلوغ المرام.

لابن عثيمين (4/ 631).

منحة العلام في شرح بلوغ المرام.

لعبد الله الفوزان (7/ 463).

عون المعبود شرح سنن أبي داود.

ومعه حاشية ابن القيم.

محمد أشرف العظيم آبادي (6/ 121).