Wanda ya shiryar a kan wani alheri, to, shi ma yana da kwatankwacin ladan wanda ya aikatashi
Daga Abu Mas'ud Al-Ansari - Allah Ya yarda da shi - ya ce:
Wani mutum ya zo wurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - sai ya ce: Tafiya ta yanke min, ka ba ni dabbar da za ta ɗaukeni, sai ya ce: "Ba ni da ita", sai wani mutum ya ce: Ya Manzon Allah, ni zan shiryar da shi ga wanda zai ba shi dabbar da za ta ɗaukeshi, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ce: "Wanda ya shiryar a kan wani alheri, to, shi ma yana da kwatankwacin ladan wanda ya aikatashi".
جَاءَ رَجُلٌ إِلَى النَّبِيِّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ فَقَالَ: إِنِّي أُبْدِعَ بِي فَاحْمِلْنِي، فَقَالَ: «مَا عِنْدِي»، فَقَالَ رَجُلٌ: يَا رَسُولَ اللهِ، أَنَا أَدُلُّهُ عَلَى مَنْ يَحْمِلُهُ، فَقَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: «مَنْ دَلَّ عَلَى خَيْرٍ فَلَهُ مِثْلُ أَجْرِ فَاعِلِهِ».
Wani mutum ya zo ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - sai ya ce: Lallai cewa dabbata ta halaka, ka ɗorani a kan wata dabbar, kuma ka ba ni wani abin hawan da zai kai ni, sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ba shi uzuri cewa ba shi da wani abin da zai dorashi a kansa, sai wani mutum da ya ke wurin ya ce: Ya Manzon Allah, ni zan shiryar da shi ga wanda zai ba shi dabbar da za ta ɗaukeshi, sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ba da labarin cewa ya zama abokin tarayyar mai sadakar a lada; domin ya shiryar da mabuƙacin zuwa gareshi.
...:
Kwaɗaitarwa a kan shiryarwa ga aikin alheri.
Kwaɗaitarwa ga aikata alheri yana daga sabubban taimakekeniya ga zamantakewa da kuma cikarsa.
Yalwar falalar Allah - Maɗaukakin sarki -.
Hadisin ƙa'ida ne mai gamewa, yana shiga kowa ne ayyukan alheri.
Idan mutum bai sami damar tabbatar da buƙatar mai tambaya ba, to, ya shiryar da shi ga waninsa.
Sahih Muslim (3/ 1506) (1893).
Kari (5)
شرح النووي على مسلم (11/ 166).
توضيح الأحكام من بلوغ المرام.
للبسام (7/ 349).
فتح ذي الجلال والاكرام بشرح بلوغ المرام.
لابن عثيمين (6/ 298).
An ambata a cikin littattafai
6 Littattafai- TABBATACCAN BAYYANI A KAN YAWANCIN MAS'ALOLIN HAJJI DA UMRA DA KUMA ZIYARA A KAN DORON LITTAFI DA SUNNAHالتحقيق والإيضاح لكثير من مسائل الحج والعمرة والزيارة - النسخة المعتمدة«Duk wanda ya shiryar akan wani aikin alheri, to, yana da kwatankwacin ladan wanda ya aikata shi ([141)»
- ABIN ZABOWA DAGA ABIN KASUWANCI MAI RIBA A CIKIN LADAN AIKI NA GARIالمنتقى من المتجر الرابح في ثواب العمل الصالح"Duk wanda ya shiryar akan wani aikin alheri, to, yana da kwatankwacin ladan wanda ya aikata shi".
Kari (4)
- الدعوة إلى الله وأخلاق الدعاة«مَنْ دَلَّ عَلَى خَيْرٍ فَلَهُ مِثْلُ أَجْرِ فَاعِلِهِ »
- تحفة الأخيار تحفة الأخيار (ببيان جملة نافعة مما ورد في الكتاب والسنة من الأدعية والأذكار)«مَنْ دَلَّ عَلَى خَيْرٍ فَلَهُ مِثْلُ أَجْرِ فَاعِلِهِ» [102]
- رياض الصالحينرياض الصالحين مع فوائد وهدايات - 1 «مَنْ دَلَّ عَلَىٰ خَيْرٍ فَلَهُ مِثْلُ أَجْرِ فَاعِلِهِ»،
- رياض الصالحينرياض الصالحين مع فوائد وهدايات - 2«مَنْ دَلَّ عَلَىٰ خَيْر فَلَهُ مِثْلُ أَجْرِ فَاعِلِهِ».