Skip to content
القَصَص /

Aya 56

28 : 56

Aya 56 of القَصَص (28 : 56). This page carries the verse in the Uthmani script with a translation of its meaning, at a stable URL that can be cited on its own.

القَصَص Ayoyi 88
28 : 56

إِنَّكَ لَا تَهۡدِي مَنۡ أَحۡبَبۡتَ وَلَٰكِنَّ ٱللَّهَ يَهۡدِي مَن يَشَآءُۚ وَهُوَ أَعۡلَمُ بِٱلۡمُهۡتَدِينَ

Lalle ne kai bã ka shiryar da wanda ka so, amma kuma Allah Yanã shiryar da wanda Yake so, kuma Shi ne Mafi sani daga mãsu shiryuwa.

Explanation & meanings · 1
  1. Annabi, tsĩra da aminci su tabbata a gare shi, ya kasance yanã son mutãnensa Ƙuraishãwa su shiryu har dai Amminsa Abu Talib, sai Allah Ya gaya masa cewa shiriya ga hannunsa take, shi kaɗai, kuma sai wanda Ya so, shi ne zai shiryu, amma kuma akwai daga cikin dalĩlai bayyanannu maganar hijira kamar yadda ãyar da ke tafe ta bayyana.