Skip to content
البَقَرَة /

Aya 224

2 : 224

Aya 224 of البَقَرَة (2 : 224). This page carries the verse in the Uthmani script with a translation of its meaning, at a stable URL that can be cited on its own.

البَقَرَة Ayoyi 286
2 : 224

وَلَا تَجۡعَلُواْ ٱللَّهَ عُرۡضَةٗ لِّأَيۡمَٰنِكُمۡ أَن تَبَرُّواْ وَتَتَّقُواْ وَتُصۡلِحُواْ بَيۡنَ ٱلنَّاسِۚ وَٱللَّهُ سَمِيعٌ عَلِيمٞ

Kuma kada ku sanya Allah kambu ga rantsuwõyinku dõmin kada ku yi wani alhẽri, kuma ku yi taƙawa, kuma ku yi wani gyara tsakãnin mutãne, kuma Allah Mai jĩ ne, Masani.

Explanation & meanings · 1
  1. Bãyanin rantsuwa da hukunce-hukuncenta. Kada ku sanya rantsuwa da Allah sababin rashin aikata wani alheri, kõ wani aikin ɗã'a, kõ kuma sanya sulhu a tsakanin mutãne, kamar a rõƙe shi ga wani abu daga cikinsu, sai ya yi rantsuwa ya ce: "Wallãhi bã zan yi ba," dõmin tsare kansa daga aikatãwar abin da aka nema gare shi. Yin irin wannan rantsuwa makarũhi ne kõ haram, gwargwadon nauyin abin da aka yi ta sabõda rashin yin sa. Kambu shi ne wurin gwada harbi.