Skip to content
البَقَرَة /

Aya 223

2 : 223

Aya 223 of البَقَرَة (2 : 223). This page carries the verse in the Uthmani script with a translation of its meaning, at a stable URL that can be cited on its own.

البَقَرَة Ayoyi 286
2 : 223

نِسَآؤُكُمۡ حَرۡثٞ لَّكُمۡ فَأۡتُواْ حَرۡثَكُمۡ أَنَّىٰ شِئۡتُمۡۖ وَقَدِّمُواْ لِأَنفُسِكُمۡۚ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَٱعۡلَمُوٓاْ أَنَّكُم مُّلَٰقُوهُۗ وَبَشِّرِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ

Mãtanku gõnaki ne a gare ku, sabõda haka ku je wa gõnakinku yadda kuka so. Kuma ku gabãtar (da alheri) sabõda kanku, ku bi Allah da taƙawa. Kuma ku sani cẽwa lalle nekũ mãsu haɗuwa da Shi ne. Kuma ka bãyar da bishãra ga mũminai.

Explanation & meanings · 1
  1. Mutum na iya sãduwa da mãtarsa yadda yake so kuma yadda ya sauƙaƙa a gare shi, daga gaba kõ daga bãya, amma ga farji banda ga dubura. Ma'anar ku gabãtar da alheri dõmin rãyukanku, shi ne ku yi basmala ku nemi tsari daga Shaiɗan sabõda 'ya'yanku. Ba a jimã'i da mace alhãli tanã barci, ana son gabãtarda wãsa.