Skip to content
البَقَرَة /

Aya 225

2 : 225

Aya 225 of البَقَرَة (2 : 225). This page carries the verse in the Uthmani script with a translation of its meaning, at a stable URL that can be cited on its own.

البَقَرَة Ayoyi 286
2 : 225

لَّا يُؤَاخِذُكُمُ ٱللَّهُ بِٱللَّغۡوِ فِيٓ أَيۡمَٰنِكُمۡ وَلَٰكِن يُؤَاخِذُكُم بِمَا كَسَبَتۡ قُلُوبُكُمۡۗ وَٱللَّهُ غَفُورٌ حَلِيمٞ

Allah ba Ya kãmã ku da laifi sabõda yãsasshiya a cikin rantsuwõyinku. Kuma amma Yana kama ku sabõda abin da zukãtanku suka sanã'anta. Kuma Allah Mai gãfara ne, Mai haƙuri.

Explanation & meanings · 1
  1. Yasasshiyar rantsuwa ita ce, a wurin Mãlik, rantsuwa a kan abin da mutum ke ganin sa tabbatacce ne, sai ya bayyana daga bãya akasin tunãninsa. Kamar ya ce Wallãhi bã ni da kuɗi, ga saninsa kuwa haka ne bã ya da su, bai sani ba ashe wani yã mutu, yã yi gãdo. A Shafi'i ita ce: ã'aha Wallahi, I, wallãhi, a cikin magana bã da nufi ba.