Wanda ya kiyaye akan raka'o'i huɗu kafin azahar da huɗu a bayanta Allah Zai haramta wuta gare shi
Daga Ummu Habiba - Allah Ya yarda da ita - matar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ta ce: Na ji Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana cewa:
"Wanda ya kiyaye akan raka'o'i huɗu kafin azahar da huɗu a bayanta Allah Zai haramta wuta gare shi ".
«مَنْ حَافَظَ عَلَى أَرْبَعِ رَكَعَاتٍ قَبْلَ الظُّهْرِ وَأَرْبَعٍ بَعْدَهَا حَرَّمَهُ اللَّهُ عَلَى النَّارِ».
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi wa wanda ya yi sallar nafila raka'a huɗu kafin sallar Azahar, da raka'o'i huɗu a bayanta albishir, kuma ya dawwama ya kiyaye akansu (cewa) Allah Zai haramta wuta gare shi .
An so kiyayewa akan raka'o'i huɗu kafin Azahar da (raka'o'i) huɗu a bayanta.
Salloli ratibai kafin sallah - wato kafin farillah -; suna da hikimomi, daga cikinsu: Yi wa zuciyar mai sallah tanadi ga ibada kafin shiga cikin farilla, amma na bayan sallah daga cikin hikimominsu akwai gyara kuskure a farillai.
Akwai fa'idoji da yawa a (salloli) ratibai, na ƙarin kyawawan ayyuka, da kankare munanan ayyuka, da ɗaga darajoji.
Ka'idojin Ahlus Sunnah a cikin hadisan alkawari irin wannan hadisin: Ita ce a ɗauki (hadisan) akan mutuwa akan tauhidi, kuma cewa abin nufi rashin dawwama a cikin wuta; domin mai aikata zunubai cikin masu tauhidi ya cancanci uƙuba sai dai ba zai dawwama a cikin wuta ba in an yi masa uƙuba.
Sunan Abi Dawud (2/ 448) (1269).
Sunan Tirmizi (1/ 452) (428).
Sunanu Nasa'i (3/ 265) (1816).
Sunanu Ibn Majah (2/ 238) (1160).
Musnad Ahmad (44/ 358) (26772).
Kari (4)
سبل السلام شرح بلوغ المرام.
لمحمد الصنعاني (1/ 336).
توضيح الأحكام مِن بلوغ المرام.
لعبد الله البسام (2/ 381).