Skip to content

Idan zaka yi sujjada, to ka sanya tafukanka ka kuma ɗaga gwiwowin hannunka

Daga Bara'u - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce -:

"Idan zaka yi sujjada, to ka sanya tafukanka ka kuma ɗaga gwiwowin hannunka".

«إِذَا سَجَدْتَ، فَضَعْ كَفَّيْكَ وَارْفَعْ مِرْفَقَيْكَ».

Muslim ne ya rawaito shi
Ingantacce ne
Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana halin hannaye a cikin sujjadar sallah, hakan da ya tabbatar da tafukansa a ƙasa kuma ya ɗora yatsun a ɗunƙule a fuskantar alƙibla, kuma gwiwowin hannaye - sune mararrabar zira'i da damutse - a ɗage daga taɓ ƙasa kuma a buɗe daga sasanni.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

Wajibi akan mai sallah ya ɗora tafukansa akan ƙasa, tafuka biyu gaɓɓai ne daga gaɓɓan sujjada guda bakwai.

An so ɗaga zira'i biyu daga ƙasa, da karhancin shinfiɗasu kamar yadda zaki yake shinfiɗa zira'ansa biyu.

Halaccin bayyanar da nishaɗi da ƙarfi da kwaɗayi a cikin ibada.

Mai yin sallah idan ya dogara akan dukkan gaɓɓan sujjada, to kowace gaɓa zata riƙi haƙƙinta na ibada.

Manazarta

Sahih Muslim (1/ 356) (494).

Kari (6)

سبل السلام شرح بلوغ المرام.

لمحمد الصنعاني (1/ 273).

توضيح الأحكام مِن بلوغ المرام.

لعبد الله البسام (2/ 235).

تيسير العلام شرح عمدة الأحكام.

لعبد الله البسام (ص162).