Skip to content

Ku yawaita tina mai rushe jin daɗi". Yana nufin mutuwa

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:

"Ku yawaita tina mai rushe jin daɗi". Yana nufin mutuwa.

«أَكْثِرُوا ذِكْرَ هَادمِ اللَّذَّاتِ» يَعْنِي الْمَوْتَ.

Tirmizi da Nasa'i da Ibnu Majah ne Suka Rawaito shi
Hasan ne
Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kwaɗaitar akan yawaita tinanin mutuwa, da tinaninta ne mutum yake tuna lahira, kuma soyayyarsa ga duniya ta rushe a cikin zuciyarsa, musammanma dai abubuwan da aka haramta.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

Mutuwa tana yanke jin daɗin duniya, sai dai a haƙƙin mumini tana dago shi zuwa jin daɗin lahira da jin daɗin aljanna da abinda yake faruwa a cikinta na alheri mai girma.

Tina mutuwa da abinda ke bayanta yana daga sabubban tuba da barin laifi da kuma tanadi dan lahira.

Manazarta

Sunan Tirmizi (4/ 141) (2307).

Sunanu Nasa'i (4/ 4) (1824).

Sunanu Ibn Majah (5/ 326) (4258).

Kari (1)

ذخيرة العقبى في شرح المجتبى (18/ 219).