To ku haɗu akan abincinku, kuma ku ambaci sunan Allah akansa, za'a sanya muku albarka a cikinsa
Daga Wahshi ɗan Harb - Allah Ya yarda da shi -:
Cewa su sun ce: Ya Manzon Allah, lallai mu mun kasance muna ci ba ma ƙoshi, ya ce: «Wataƙila kuna ci ne a rarrabe?» Ya ce: Eh. Ya ce: «To ku haɗu akan abincinku, kuma ku ambaci sunan Allah akansa, za'a sanya muku albarka a cikinsa».
أَنَّهُمْ قَالُوا: يَا رَسُولَ اللَّهِ، إِنَّا نَأْكُلُ وَلَا نَشْبَعُ، قَالَ: «فَلَعَلَّكُمْ تَأْكُلُونَ مُتَفَرِّقِينَ؟» قَالُوا: نَعَمْ. قَالَ: «فَاجْتَمِعُوا عَلَى طَعَامِكُمْ، وَاذْكُرُوا اسْمَ اللَّهِ عَلَيْهِ، يُبَارَكْ لَكُمْ فِيهِ».
Wasu daga cikin sahabbai sun tambayi Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sai suka ce: Lallai mu mun kasance muna ci amma bama ƙoshi. Sai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce musu: Wataƙila kuna rarrabuwa a lokacin ci; sai kowa ya ci shi kaɗai? Suka ce: Eh. Ya ce: To ku haɗu ku ci ba'a rarrabe ba, kuma ku ambaci sunan Allah a lokacin ci da faɗin: Bismillah (Da sunan Allah), za'a sanya muku albarka a cikinsa, kuma zaku ƙoshi.
Haɗuwa a abinci da kuma ambatan Allah a lokacin ci sababi ne na samun albarka a cikin abinci, da kuma ƙoshi daga cinsa.
Rabuwa dukkaninta sharri ce, haɗuwa kuwa dukkaninta alheri ce.
Kwaɗaitarwa akan haɗuwa da kuma ambatan Allah a lokacin abinci.
Sindi ya ce: Da haɗuwa ne albarkatu suke sauka a cikin abin ci, kuma da ambatan Allah ne Shaiɗan yake hanuwa daga kaiwa ga abinci.
Sunan Abi Dawud (5/ 588) (3764).
Sunanu Ibn Majah (4/ 418) (3286).
Musnad Ahmad (25/ 485) (16078).
Kari (6)
شرح رياض الصالحين.
لابن عثيمين (4/ 217).
نزهة المتقين بشرح رياض الصالحين.
لمجموعة من الباحثين (1/ 607).
بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين.
لسليم الهلالي (2/ 59).