Idan kun ji ladani; to, ku faɗi irin abin da yake faɗa, sannan ku yi min salati
Daga Abdullahi ɗan Amr ɗan Aas - Allah Ya yarda da su - cewa ya ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa:
"Idan kun ji ladani; to, ku faɗi irin abin da yake faɗa, sannan ku yi min salati, domin cewa wanda ya yi min salati ɗaya Allah zai yi masa salati goma da shi, sannan ku roƙi Allah Wasila gareni, domin cewa ita wani matsayi ne a aljanna, ba ya kamata sai ga wani bawa daga bayin Allah, ina ƙaunar in zama ni ne shi, duk wanda ya roƙi Allah Wasila gareni, to, cetona zai tabbata gare shi".
«إِذَا سَمِعْتُمُ الْمُؤَذِّنَ فَقُولُوا مِثْلَ مَا يَقُولُ، ثُمَّ صَلُّوا عَلَيَّ، فَإِنَّهُ مَنْ صَلَّى عَلَيَّ صَلَاةً صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ بِهَا عَشْرًا، ثُمَّ سَلُوا اللهَ لِيَ الْوَسِيلَةَ، فَإِنَّهَا مَنْزِلَةٌ فِي الْجَنَّةِ، لَا تَنْبَغِي إِلَّا لِعَبْدٍ مِنْ عِبَادِ اللهِ، وَأَرْجُو أَنْ أَكُونَ أَنَا هُوَ، فَمَنْ سَأَلَ لِيَ الْوَسِيلَةَ حَلَّتْ لَهُ الشَّفَاعَةُ».
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya nuna wa wanda ya ji mai kiran sallah da ya maimaita a bayansa, sai ya faɗi irin abinda ya fada, ban da Hai'ala biyu, cewa ya ce a bayansu: Babu dabara ba ƙarfi sai ga Allah. Sannan ya yi salati ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - bayan gama kiran sallah, domin cewa wanda ya yi salati ɗaya a gare shi to Allah zai yi masa salati goma da shi, ma'anar salatin Allah ga bawanSa: shi ne YabonSa ga bawa a wurin Mala'iku. Sannan ya yi umarni da a roƙa masa Allah Wasila - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -, ita ɗin wani matsayi ne a aljanna, shi ne mafi ƙololuwa, ba ta dace ba, kuma wannan matsayin ba zai samu ba sai ga wani bawa ɗaya daga dukkanin bayin Allah - Maɗaukakin sarki -, ina ƙaunar in zama ni ne shi, kaɗai (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya faɗa ne, don Tawalu’u; domin cewa idan shi wannan matsayin da yake babba ba zai kasance ba sai ga mutum ɗaya, to, ai wannan mutum ɗayan ba zai zama ba sai shi (Annabin) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi; domin shi ne mafificin halitta. Sannan (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya bayyana cewa wanda ya roƙa wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - Wasila; to, cetonsa zai same shi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -.
...:
Kwaɗaitarwa a kan amsawa mai kiran sallah.
Falalar salati ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - bayan amsawa mai kiran sallah
Kwaɗaitarwa a kan roƙa wa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - Wasila bayan salati a gareshi .
Bayanin ma'anar Wasila, da ɗaukakar darajarta ta inda ba ta tabbata sai ga wani bawa ɗaya.
Bayanin falalar Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yayin da aka keɓanceshi da wancan babban matsayin.
Wanda ya roƙi Allah Wasila ga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - to, cetonsa zai ya halatta gare Shi.
Bayanin ƙanƙar da kansa - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yayin da ya nemi addu'a daga al'ummarsa na wannan matsayin, tare da cewa zai kasance gare shi.
Yalwar falalar Allah da rahamarSa, aikin lada ɗaya (za a yi sakamako) da goma tamkarta.
Sahih Muslim (1/ 288) (384).
Kari (2)
البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (9/ 111 (9/ 109).
المفهم لما أشكل من تلخيص كتاب مسلم (2/ 13).
An ambata a cikin littattafai
20 Littattafai- TAƘAITACCEN BAYANI MAI AMFANI GA LADAN DA LIMAN DA MAI HUDUBA DA KUMA HUKUNCE HUKUNCEN MASALLACI«Idan kun ji ladani; to, ku faɗi irin abin da yake faɗa, sannan ku yi min salati, domin duk wanda ya yi min salati ɗaya Allah zai yi masa salati goma da shi, sannan ku roƙi Allah Wasila gareni, domin cewa ita wani matsayi ne a aljanna, ba y
- ABIN ZABOWA DAGA ABIN KASUWANCI MAI RIBA A CIKIN LADAN AIKI NA GARIالمنتقى من المتجر الرابح في ثواب العمل الصالح"Idan kun ji ladani, to, ku faɗi irin abin da ya ke faɗa, sannan ku yi salati a gare ni, domin cewa wanda ya yi salati a gare ni salati ɗaya Allah zai yi salati goma a gare shi sabo da shi, sannan ku roƙa min Allah Al-Wasila, domin cewa ita
Kari (18)
- الخطب المنبريةموسوعة الخطب المنبرية (القسم الأول)«مَن صَلَّى عَلَيَّ صَلَاةً صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ بِهَا عَشْرًا»
- الخطب المنبرية موسوعة الخطب المنبرية (القسم الثاني)«مَنْ صَلَّىٰ عَلَيَّ صَلَاةً صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ بِهَا عَشْرًا»
- الخطب المنبريةموسوعة الخطب المنبرية (القسم الثالث)«مَنْ صَلَّى عَلَيَّ صَلَاةً صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ بِهَا عَشْرًا»
- الخطب المنبريةموسوعة الخطب المنبرية (القسم الثالث)«مَنْ صَلَّى عَلَيَّ صَلَاةً صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ بِهَا عَشْرًا»
- الذكر والدعاء والعلاج بالرقي من الكتاب والسنة"من صلى عليَّ صلاة صلى الله عليه بها عشراً" .
- الصلاة التي علمها النبي ﷺ الصحابة رضي الله عنهمالصلاة التي علمها النبي ﷺ الصحابة رضي الله عنهم«إِذَا سَمِعْتُمُ الْمُؤَذِّنَ، فَقُولُوا مِثْلَ مَا يَقُولُ ثُمَّ صَلُّوا عَلَيَّ، فَإِنَّهُ مَنْ صَلَّى عَلَيَّ صَلَاةً صَلَّى الله عَلَيْهِ بِهَا عَشْرًا، ثُمَّ سَلُوا اللهَ لِيَ الْوَسِيلَةَ، فَإِنَّهَا مَنْزِلَةٌ فِي الْجَنَّةِ، لَا تَ
- الصلاة التي علمها النبي ﷺ الصحابة رضي الله عنهم«إِذَا سَمِعْتُمُ الْمُؤَذِّنَ، فَقُولُوا مِثْلَ مَا يَقُولُ ثُمَّ صَلُّوا عَلَيَّ، فَإِنَّهُ مَنْ صَلَّى عَلَيَّ صَلَاةً صَلَّى الله عَلَيْهِ بِهَا عَشْرًا، ثُمَّ سَلُوا اللهَ لِيَ الْوَسِيلَةَ، فَإِنَّهَا مَنْزِلَةٌ فِي الْجَنَّةِ، لَا تَ
- المختصر المفيد للمسلم(من صلى عليّ صلاة صلى الله عليه بها عشرا)
- تحفة الأخيار تحفة الأخيار (ببيان جملة نافعة مما ورد في الكتاب والسنة من الأدعية والأذكار)«إِذَا سَمِعْتُمُ الْمُؤَذِّنَ، فَقُولُوا مِثْلَ مَا يَقُولُ ثُمَّ صَلُّوا عَلَيَّ، فَإِنَّهُ مَنْ صَلَّى عَلَيَّ صَلَاةً صَلَّى الله عَلَيْهِ بِهَا عَشْرًا، ثُمَّ سَلُوا اللهَ لِيَ الْوَسِيلَةَ، فَإِنَّهَا مَنْزِلَةٌ فِي الْجَنَّةِ، لَا تَ
- حصن المسلم من أذكار الكتاب والسنةحصن المسلم«مَنْ صَلَّى عَلَيَّ صَلَاةً صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ بِهَا عَشْرًا»[265].
- رسالة في الأذكار1«إِذَا سَمِعْتُمُ المُؤَذِّنَ فَقُولُوا مِثْلَ مَا يَقُولُ، ثُمَّ صَلُّوا عَلَيّ؛ فَإِنَّهُ مَنْ صَلَّى عَلَيّ صَلَاةً صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ بِهَا عَشْرًا، ثُمَّ سَلُوا اللهَ لِيَ الْوَسِيلَةَ؛ فَإِنَّهَا مَنْزِلَةٌ فِي الجَنَّةِ لَا تَنْبَ
- رسالة في الأذكار1«مَنْ صَلَّى عَلَيَّ صَلَاةً صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ بِهَا عَشْرًا».
- رياض الصالحينرياض الصالحين مع فوائد وهدايات - 5«إذا سَمِعْتُمُ المُؤَذِّنَ فَقُولُوا مِثْلَ مَا يَقُولُ، ثُمَّ صَلُّوا عَلَيَّ، فَإنَّهُ مَنْ صلَّىٰ عَلَيَّ صلاةً صَلَّىٰ اللهُ عَلَيْهِ بِهَا عَشْراً، ثُمَّ سَلُوا اللهَ لِيَ الْوَسِيلَةَ، فَإنَّهَا مَنْزِلَةٌ في الجَنَّةِ لا تَنْبَغِي إ
- رياض الصالحينرياض الصالحين مع فوائد وهدايات - 7«مَنْ صلَّىٰ عليَّ صلاةً صلَّىٰ اللهُ عليه بها عَشْراً».
- مجموعة زاد التربية الإسلامية (1)، والسيرة النبوبة (1)، والعقيدة (1)، والفقه (1)2«من صلى عليَّ صلاةً صلّى الله عليه بها عشرًا».
- مجموعة زاد التربية الإسلامية (1)، والسيرة النبوبة (1)، والعقيدة (1)، والفقه (1)مجموعة زاد الفقه (1)«إِذَا سَمِعْتُمْ الْمُؤَذِّنَ فَقُولُوا مِثْلَ مَا يَقُولُ ثُمَّ صَلُّوا عَلَيَّ، فَإِنَّهُ مَنْ صَلَّى عَلَيَّ صَلَاةً صَلَّى الله عَلَيْهِ بِهَا عَشْراً، ثُمَّ سَلُوا الله لِي الْوَسِيلَةَ فَإِنَّهَا مَنْزِلَةٌ فِي الْجَنَّةِ لَا تَنْبَغ
- مشروع منهاج زادكزادك 3 طالب نهائي«مَنْ صَلَّى عَلَيَّ صَلَاةً صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ بِهَا عَشْرًا»
- نبراس طالب (1)1«مَنْ صَلَّى عَلَيَّ صَلَاةً صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ بِهَا عَشْرًا»