Skip to content

Lalle Allah Yana yarda da bawanda idan ya ci abin ci, yana gode masa a kai, ko in ya sha abin sha sai ya gode masa akan hakan

Daga Anas Ɗan Malik - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce:

Lalle Allah Yana yarda da bawanda idan ya ci abin ci, yana gode masa a kai, ko in ya sha abin sha sai ya gode masa akan hakan.

«إِنَّ اللهَ لَيَرْضَى عَنِ الْعَبْدِ أَنْ يَأْكُلَ الْأَكْلَةَ فَيَحْمَدَهُ عَلَيْهَا، أَوْ يَشْرَبَ الشَّرْبَةَ فَيَحْمَدَهُ عَلَيْهَا».

Muslim ne ya rawaito shi
Ingantacce ne
Bayani

Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana bayyana godiyar da bawa ya ke yi wa Ubangijinsa a kan falalarSa da ni’imarSa suna cikin al’amuran da ake samun yardar Allah da su, idan ya ci abin ci sai ya ce: Na gode wa Allah. Idan ya sha abin sha sai ya ce: Alhamdulillah.

Ma"anonin Kalmomi

...:

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

Karamcin Allah Mabuwayi, haƙiƙa shi ne ya ba da arziƙi, kuma yake yarda da a gode masa.

Yardar Allah ana samunta da abu mafi sauƙi, kamar godiya ga Allah bayan ci da sha.

Yana daga cikin ladubban ci da sha: Godiya ga Allah maɗaukaki bayan ci da sha.

Manazarta

Sahih Muslim (4/ 2095) (2734).

Kari (10)

نزهة المتقين شرح رياض الصالحين.

لمصطفى الخن وغيره (1/ 164).

بهجة الناظرين شرح رياض الصالحين.

لسليم الهلالي (1/ 215).

شرح رياض الصالحين من كلام سيد المرسلين.

لابن عثيمين (2/ 203).

كنوز رياض الصالحين.

لمجموعة من الباحثين.

تطرز رياض الصالحين.

لفيصل آل مبارك (ص764).