Skip to content

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan zai shiga bandaki zai ce: "Ya Allah ni ina neman tarinKa daga Shaidanu maza da Shaidanu mata

Daga Anas - Allah Ya yarda da shi - ya ce:

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan zai shiga bandaki zai ce: "Ya Allah ni ina neman tarinKa daga Shaidanu maza da Shaidanu mata".

كَانَ النَّبِيُّ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ إِذَا دَخَلَ الخَلاَءَ قَالَ: «اللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنَ الخُبُثِ وَالخَبَائِثِ».

Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya kasance idan ya yi nufin shiga gurin da zai biya bukatarsa a cikinsa, fitsarine ko bayan gida, zai nemi tsarin Allah, kuma zai fake gareShi da ya kareShi daga sharrin Shaidanu maza da mata, An fassara khubs da kahaba'is kuma da sharri da kuma najasa.

Ma"anonin Kalmomi

...:

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

An so yin wannan addu'ar a yayin nufin shiga bandaki.

Dukkanin halitta masu bukatuwa ne zuwa Ubangijinsu na a tunkude abinda yake cutar da su a kowanne yanayi.

Manazarta

Sahih Al-Bukhari (1/ 40) (142).

Sahih Muslim (1/ 283) (375).

Kari (4)

الإلمام بشرح عمدة الأحكام.

لإسماعيل الأنصاري (1/ 23).

تيسير العلام شرح عمدة الأحكام.

للبسام (ص36).