Skip to content

Lallai tsakanin mutum da shirka da kafirci (shi ne) barin sallah

Daga Jabir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Na ji Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana cewa:

"Lallai tsakanin mutum da shirka da kafirci (shi ne) barin sallah".

«إِنَّ بَيْنَ الرَّجُلِ وَبَيْنَ الشِّرْكِ وَالْكُفْرِ تَرْكَ الصَّلَاةِ».

Muslim ne ya rawaito shi
Ingantacce ne
Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi gargaɗi game da barin sallar farilla, ya ba da labarin cewa tsakanin mutum da afkawa a shirka da kafirci (shi ne) barin sallah, sallah ita ce rukuni na biyu daga rukunan musulunci, al'amarinta mai girma ne a musulunci, wanda ya barta yana mai musun wajabcinta, to, ya kafirta da ijima'in musulmai, idan ya barta gabaɗaya don wulaƙantarwa da kasala, to, shi kafiri ne, an cirato ijma'in sahabbai a kan hakan, idan ya kasance yana bari wani lokaci wani lokaci kuma yana yin sallah, to, ya kai kansa ga wannan narkon mai tsanani.

Ma"anonin Kalmomi

...:

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

Muhimmancin sallah da kiyayewa a kanta, ita ce mai banbanta wa tsakanin kafirci da imani.

Gargaɗi mai tsanani a kan barin sallah da tozartata.

Manazarta

Sahih Muslim (1/ 88) (82).

Kari (2)

المفهم لما أشكل من تلخيص كتاب مسلم (1/ 271).

البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (2/ 622).