Skip to content

Babu sallah ga wanda bai karanta Fatiha ba

Daga Ubadah dan Samit - Allah Ya yarda da shi - cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce:

"Babu sallah ga wanda bai karanta Fatiha ba".

«لَا صَلَاةَ لِمَنْ لَمْ يَقْرَأْ بِفَاتِحَةِ الكِتَابِ».

Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Ingantacce ne
Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa sallah ba ta inganta sai da karanta suratul Fatiha, ita rukuni ce daga rukunan sallah a kowace raka'a.

Ma"anonin Kalmomi

...:

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

Wanin karatun Fatiha ba ya isarwa daga gareta tare da iko a kanta.

Bacin raka'ar da ba'a karanta Fatiha a cikinta ba, daga mai ganganci da jahili da mai mantuwa; Domin cewa ita rukuni ce, rukunai ba sa saraya ta kowanne hali.

Karatun Fatiha yana saraya daga mamu idan ya riski liman yana ruku'u.

Manazarta

Sahih Al-Bukhari (1/ 151) (756).

Sahih Muslim (1/ 295) (394).

Kari (4)

تيسير العلام.

للبسام (ص171).

تنبيه الأفهام.

لابن عثيمين (217).