Skip to content
التوبَة /

Aya 65

9 : 65

Aya 65 of التوبَة (9 : 65). This page carries the verse in the Uthmani script with a translation of its meaning, at a stable URL that can be cited on its own.

التوبَة Ayoyi 129
9 : 65

وَلَئِن سَأَلۡتَهُمۡ لَيَقُولُنَّ إِنَّمَا كُنَّا نَخُوضُ وَنَلۡعَبُۚ قُلۡ أَبِٱللَّهِ وَءَايَٰتِهِۦ وَرَسُولِهِۦ كُنتُمۡ تَسۡتَهۡزِءُونَ

Kuma lalle ne, idan ka tambaye, su haƙĩƙa, sunã cẽwa, "Abin sani kawai, mun kasance munã hĩra kuma munã wãsã. Ka ce: "Shin da Allah, da kuma ãyõyinSa da ManzonSa kuka kasance kunã izgili?"

Explanation & meanings · 1
  1. Ana a cikin tafiya zuwa Tabũka sai wasu mutãne daga cikin munãfukai suka ce wa junansu, "Wannan Yana zaton ya ci gidajen Rumawa da Biranensu? faufau." Sai Allah Ya sanar da AnnabinSa (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) abin da suka faɗa. Sai ya ce: "Ku zo mani da waɗannan mutãne." Da suka je masa ya ce musu 'Kun ce kaza da kaza.' Sai suka yi rantsuwa da cewa: ba mu kasance ba sai muna hĩra muna wãsã.