Skip to content
الحُجُرَات /

Aya 1

49 : 1

Aya 1 of الحُجُرَات (49 : 1). This page carries the verse in the Uthmani script with a translation of its meaning, at a stable URL that can be cited on its own.

الحُجُرَات Ayoyi 18
49 : 1

يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تُقَدِّمُواْ بَيۡنَ يَدَيِ ٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦۖ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَۚ إِنَّ ٱللَّهَ سَمِيعٌ عَلِيمٞ

Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku gabãta (da kõme) gaba ga Allah da Manzon Sa. Kuma ku yi ɗã'ã ga Allah da taƙawa. Lalle Allah Mai ji ne, Masani.

Explanation & meanings · 1
  1. Wannan yã nũna mana cewa bã yã halatta ga Musulmi ya yi wani aiki ko ya faɗi wata magana sai yã san hukuncin Allah a cikinsu. Kuma kada ya ƙãra wãyõnsa a kan abinda Allah Yã ce, kuma kada ya rage idan yanã da ĩkon cikãwa. Dukan wannan yakan ja Musulmi ga ɓãcin ayyukansa, watau ya yi ridda daga Musulunci.