Skip to content
البَقَرَة /

Aya 168

2 : 168

Aya 168 of البَقَرَة (2 : 168). This page carries the verse in the Uthmani script with a translation of its meaning, at a stable URL that can be cited on its own.

البَقَرَة Ayoyi 286
2 : 168

يَٰٓأَيُّهَا ٱلنَّاسُ كُلُواْ مِمَّا فِي ٱلۡأَرۡضِ حَلَٰلٗا طَيِّبٗا وَلَا تَتَّبِعُواْ خُطُوَٰتِ ٱلشَّيۡطَٰنِۚ إِنَّهُۥ لَكُمۡ عَدُوّٞ مُّبِينٌ

Yã ku mutãne! Ku ci daga abin da yake a cikin ƙasa, wanda yake halal, mai dãɗi. Kuma kada ku bi zambiyõyin Shaiɗan. Lalle ne shi, gare ku, maƙiyi ne bayyananne.

Explanation & meanings · 2
  1. Yã kira mutãne a nan, bai ce mũminai ba, dõmin ba dukan Musulmi yake mũmini ba, sai wanda ya tsĩra daga ãyõyin da ke tafe. A cikinsu akwai abin da zai mai da Musulmi kãfiri kõ mai bidi'a.
  2. Hanyõyin Shaiɗan ga halattar da abin da Allah Ya haramta kõ haramtar da abin da Allah Ya halatta dõmin kãga hukuncin da bai zo daga Allah ba, shirka ne tãre da Allah. Yã ce zambiyõyin Shaiɗan, dõmin Shaiɗan bã ya da hanya miƙaƙƙiya.