Skip to content

Idan akace dakai menene rukunnan Imani

السؤال

?Tambaya: Idan akace dakai menene rukunnan Imani

الجواب

Amsa; sai kace: rukunan Imani guda shida ne sune: Imani da Allah, imani da mala’ikunsa imani da litattafansa, imani da manzanninsa, imani da ranar lahira da qaddara mai kyau da mara kyau duka daga Allah suke.?

kuma imani ba zai cika ba sai anyi imani dasu baki dayansu kamar yadda Alqur’ani da hadisi suka nuna, duk wanda kuma yayi musu da daya daga ciki to ya fita daga farfajiyar imani Saboda fadin Allah ta’ala: ba fuskantar gabas da yamma ne kyautayi ba, amma kyautayi shine wanda yai Imani da Allah da ranar lahira da mala’iku da littafi da annabawa sannan ya bayar da dukiya abisa yana sonta ga makusanta da ‘yanta bayi kuma ya tsayar da sallah, ya bayar da zakka, da kuma masu cika alkawarinsu da suka dauka da masu hakuri a lokacin tsanani da cuta da lokacin yaki, wadanan sune sukayi gaskiya, kuma wadannan sune masu tsoron Allah’ (Bakara 177) da kuma fadin Manzon Allah tsira da aminchin Allah a gareshi lokacin da aka tambayeshi akan imani Imani shine kayi imani da allah da mala’ikunsa da litattafansa da manzannninsa da ranar lahira, kuma kayi imani da Qaddara, alherinsa da sharrinsa