Skip to content

idan akace maka da wame abu ka san ubangijinka. ?

السؤال

Tambaya: idan akace maka da wame abu ka san ubangijinka. ?

الجواب

Amsa: sai kace: nasan ubangijine ne da ilmin day a halicce ni dashi, da kuma yanayin halittar dan Adam na yarda da, samuwar Allah da girmanshi da jin tsoronsa Hakanan na sanshi ta hanyar duba da lura da alamominsa da halittunsa, kamar yadda ya fada: ‘Daga alamomin (samuwar Allah akwai dare da wuni da rana da wata) (suratu Fussilat) sannan wadannan muhimmn halittu da suke irin wannan tsari da kuma kyawun gaske ba zai yiwu su samar dasu bayan da babu su Kenan suma dalilai ne masu karfi akan samuwar wani mai halitta, wanda yake da iko da girma da hikima Wannan yasa dukkan halitta in banda baudaddu marasa addini –suna da alaqa da mamallakinsu mai arzuta su, mai juya al’umarsu, wanda daga cikin cikin abubuwan day a halitta akwai sammai bakwai da kassai bakwai da abin da ke cikinsu da wanda ya san adalchinsu da ainihin yadda suke sai Allah, wanda yake basu komai, rayayye tsayayye, mahalicci, mai girma Allah yana cewa: ubangijinku shine Allah wanda ya halicci sammai da kasa a cikin kwana shida, sannan ya daidaita a al’arshi, shi yake sa dare ya rufe yini, yana nemansa da gaggawa, kuma da rana da wata da taurari ababan horewa ne da umarninsa, kuji da kyau duk halitta da umarni nasa ne, Albarkar allah Ubangijin talikai ta yawaita (A’araf 54)