Skip to content

Na kasance ina ganin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana yin sallama a damansa da kuma hagunsa, har ina ganin farin kundukukinsa

Daga Sa'ad - Allah Ya yarda da shi - ya ce:

Na kasance ina ganin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - yana yin sallama a damansa da kuma hagunsa, har ina ganin farin kundukukinsa.

كُنْتُ أَرَى رَسُولَ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يُسَلِّمُ عَنْ يَمِينِهِ، وَعَنْ يَسَارِهِ، حَتَّى أَرَى بَيَاضَ خَدِّهِ.

Muslim ne ya rawaito shi
Ingantacce ne
Bayani

Sa'ad Ibnu Abi Waƙas - Allah Ya yarda da shi - ya bada labarin cewa shi ya kasance yana ganin farin kundukukin (kumatun) Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - saboda tsananin waiwayensa idan zai sallame daga sallarsa a damansa a sallamar farko, haka a hagunsa a (sallama) ta biyu.

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

Halaccin kai matuƙa a cikin waiwaye zuwa ɓangaren dama da kuma ɓangaren hagu.

Halaccin sallama biyu zuwa dama da hagu.

Nawawi ya ce: Da a ce zai yi sallama biyu a damarsa ko a hagunsa ko ta ɓangaren fuskarsa, ko ta farkon a hagunsa, ta biyun kuma a damansa sallarsa ta inganta kuma sallama biyun ta tabbata, sai dai ya rasa falala ta yadda ake yinsu .

Manazarta

Sahih Muslim (1/ 409) (582).

Kari (2)

البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (13/ 99).

مرقاة المصابيح شرح مشكاة المصابيح (4 /30).