Skip to content
الحدِيد /

Aya 25

57 : 25

Aya 25 of الحدِيد (57 : 25). This page carries the verse in the Uthmani script with a translation of its meaning, at a stable URL that can be cited on its own.

الحدِيد Ayoyi 29
57 : 25

لَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا رُسُلَنَا بِٱلۡبَيِّنَٰتِ وَأَنزَلۡنَا مَعَهُمُ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡمِيزَانَ لِيَقُومَ ٱلنَّاسُ بِٱلۡقِسۡطِۖ وَأَنزَلۡنَا ٱلۡحَدِيدَ فِيهِ بَأۡسٞ شَدِيدٞ وَمَنَٰفِعُ لِلنَّاسِ وَلِيَعۡلَمَ ٱللَّهُ مَن يَنصُرُهُۥ وَرُسُلَهُۥ بِٱلۡغَيۡبِۚ إِنَّ ٱللَّهَ قَوِيٌّ عَزِيزٞ

Haƙĩƙa, lalle Mun aiko Manzannin Mu da hujjõji bayyanannu, kuma Muka saukar da Littãfi da sikẽli tãre da su dõmin mutãne su tsayu da ãdalci, kuma Mun saukar da baƙin ƙarfe, a cikinsa akwai cutarwa mai tsanani da amfãni ga mutãne, kuma dõmin Allah Ya san mai taimakon Sa da ManzanninSa a fake. Lalle ne Allah Mai ƙarfi ne, Mabuwãyi.

Explanation & meanings · 1
  1. Littafi a nan anã nufin dukkan Littattafan samã da aka bãyar a bãyan Nũhu da Ibrahĩm. Ma'auni kuma, shi ne sharĩ'ar da ke cikinsu. Baƙin ƙarfe kuwa dõmin kãyan aiki na amfãnin sana'õ'i da cũtar da ke a cikinsa na makãmai da kuma amfãnin tsaron addini da jihãdi. Littafi da ma'auni ana aiki da su wajen awon ibãdar Allah da mu'ãmalõli a tsakãnin mutãne.