Skip to content
البَقَرَة /

Aya 62

2 : 62

Aya 62 of البَقَرَة (2 : 62). This page carries the verse in the Uthmani script with a translation of its meaning, at a stable URL that can be cited on its own.

البَقَرَة Ayoyi 286
2 : 62

إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَٱلَّذِينَ هَادُواْ وَٱلنَّصَٰرَىٰ وَٱلصَّٰبِـِٔينَ مَنۡ ءَامَنَ بِٱللَّهِ وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡأٓخِرِ وَعَمِلَ صَٰلِحٗا فَلَهُمۡ أَجۡرُهُمۡ عِندَ رَبِّهِمۡ وَلَا خَوۡفٌ عَلَيۡهِمۡ وَلَا هُمۡ يَحۡزَنُونَ

Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, da waɗanda suka tũba, da Nasãra da Makarkata, wana ya yi ĩmani da Allah da Yinin Lãhira, kuma ya aikata aikin ƙwarai, to, suna da ijãrarsu a wurin Ubangijinsu, kuma bãbu tsõro a kansu, kuma ba su zama suna yin baƙin ciki ba.

Explanation & meanings · 1
  1. Waɗanda suka koma, watau Yahũdu, daga maganar Mũsa, "Mun kõma garesu" Sura ta 7 aya ta 156, kuma Makarkata, jama'a ce daga Lãrabãwa suka karkata daga addĩnin ubanninsu zuwa ga bauta wa malã'iku. A farkon Musulunci sunã cewa ga wanda ya musulunta, wai ya yi kama da su.