Skip to content

Idan mai biƙi ta samu tsarki kafin arba'in shin hajjinta ya inganta? Idan ba ta samu tsarki ba, yaya za ta yi, tare da sanin cewa ita maniyyaciyar hajjin ce?

السؤال

TAMBAYA TA 1:

Idan mai biƙi ta samu tsarki kafin arba'in shin hajjinta ya inganta? Idan ba ta samu tsarki ba, yaya za ta yi, tare da sanin cewa ita maniyyaciyar hajjin ce?

س60: إذا طهرت النّفساء قبل الأربعين فهل يصحّ حجّها؟ وإذا لم تر الطّهر فماذا تصنع، مع العلم أنها ناويةٌ الحج؟

الجواب

AMSA TA 1:

Idan mai biƙi ta samu tsarki kafin arba'in, to, sai ta yi wanka, ta yi sallah, ta aikata duk abin da mata masu tsarki suke aikatawa har ɗawafi; sabo da biƙi ba shi da iyaka mafi ƙaranci.

Amma idan ba ta ga tsarki ba, to, hajjinta ingantacce ne dai kuma, sai dai ba za ta yi ɗawafi a ka'aba ba har sai ta samu tsarki;

Sabo da Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya hana mai haila yin ɗawafi a Ka'aba, biƙi kuma kamar haila ne a wannan.

ﺟ60: إذا طهرت النّفساء قبل الأربعين فإنها تغتسل، وتصلّي، وتفعل كل ما تفعله الطاهرات حتى الطواف؛ لأن النّفاس لا حد لأقلّه.

أما إذا لم تر الطّهر فإن حجها صحيحٌ أيضًا، لكن لا تطوف بالبيت حتى تطهر؛ لأن النبي ﷺ منع الحائض من الطواف بالبيت[1]، والنّفاس مثل الحيض في هذا.

[29] تقدم تخريجه.