Skip to content

Menene ƙarshen lokacin sallar Isha'i? kuma ta yaya za'a iya sanin sa?

التصنيف الشرعي
الفقهالصلاةشروط الصلاة

السؤال

TAMBAYA TA 1:

Menene ƙarshen lokacin sallar Isha'i? kuma ta yaya za'a iya sanin sa?

س39: ما آخر وقت صلاة العشاء؟ وكيف يمكن معرفته؟

الجواب

AMSA TA 1:

Ƙarshen lokacin Isha'i shi ne rabin dare, kuma za'a san hakan ne ta hanyar raba abin da ya ke tsakanin faɗuwar rana da ɓullowar Alfijir zuwa gida biyu, rabi na farko da shi ne lokacin Isha'i ya ke ƙarewa, sai ya rage ɗaya rabin daren na ƙarshe, shi kuma ba lokacin ba ne, sai dai katanga (rabewa) ne tsakanin Isha'i da Asuba.

ﺟ39: آخر وقت العشاء منتصف الليل، ويعرف ذلك بأن يقسم ما بين غروب الشمس وطلوع الفجر نصفين، فالنّصف الأول ينتهي به وقت العشاء، ويبقى نصف الليل الآخر ليس وقتًا، بل برزخ بين العشاء والفجر.