Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

8 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
«Da a ce zaku dogara ga Allah haƙiƙanin dogaranSa, da Ya azirtaku kamar yadda yake azirta tsuntsu, yana wayar gari a yunwace ya kuma yi maraice cikinsa a cike».
Ingantacce ne Imam Ahmad da Tirmithi da Nasa'i da Ibnu Majah da Ibnu Hibban a cikin Sahihinsa da kuma Hakim ne Suka ruwaito shi
"Mai bayyanar da Alkur’ani kamar mai bayyanar da sadaka ne, mai boye Alkur’ani kamar mai boye sadaka ne".
Ingantacce ne Abu Dawud da Tirmizi da Nasa'i ne Suka Rawaito shi
Wani mutum ya zo gurin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sai ya ce: Shin kana ganin mutum ya yi yaƙi yana neman lada da yabo, me gare shi? sai Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: "Ba shi da komai". Sai ya maimaita masa sau uku, tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yana ce masa: "Ba shi da komai" sannan ya ce: "Lallai Allah ba Ya karɓar aiki sai wanda ya zama abin tsarkakewa, kuma aka nufi fuskar Allah da shi".
Ingantacce ne Nasa'i ne Ya Rawaito shi
"Canfi shirka ne, canfi shirka ne, canfi shirka ne, - sau uku -", babu wani a cikinmu saidai, saidai cewa Allah - Mai girma da daukaka - Yana tafiyar da shi da dogara (ga Allah).
Ingantacce ne Abu Dawud da Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad ne Suka Rawaito shi
"Ayyuka shida ne, mutane kuma hudu ne, akwai tabbatattu biyu. Da tamka da tamka, da kyakkyawa da tamkarta goma, da kyakkyawa da dari bakwai. Amma masu tabbatattu biyu: Wanda ya mutu ba ya taranya wani abu da Allah zai shiga Aljanna. Wanda ya mutu yana taranya wani abu da Allah zai shiga wuta. Amma tamka da tamka: Wanda ya himmantu da kyakkyawa har ya jiyar da zuciyarsa ita, kuma Allah Ya santa daga gareshi za'a rubuta masa kyakkyawa, wanda ya aikata mummuna, za'a rubuta mummuna akansa. Wanda ya aikata kyakkyawa da tamkarta goma, wanda ya ciyar da wani abu a tafarkin Allah to kyakkyawa da dari bakwai. Amma mutane akwai wanda aka yalwatawa a duniya aka kuntata masa a lahira, da kuma wanda aka kuntatawa a duniya kuma aka yalwata masa a lahira, da wanda aka kuntatawa a duniya da lahira, da wanda aka yalwatawa a duniya da lahira".
Hasan ne Ahmad ne ya rawaito shi
"Da a ce za ku dogara ga Allah haƙiƙanin dogaro, da Ya azurtaku kamar yadda yake azurta tsuntsu, yana wayar gari a yunwace kuma ya yi yammaci a ƙoshe".
Ingantacce ne Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad Suka ruwaito shi
"Lallai halal a bayyane yake kuma haram ma a bayyane yake, a tsakaninsu akwai wasu al'amura masu rikitarwa da yawa daga mutane ba sa saninsu, wanda ya kiyaye shubuhohi ya kuɓuta a addininsa da mutuncinsa, wanda ya afka cikin shubuhohi ya afka a cikin haram, kamar mai kiwo ne da yake kiwo a gefen shinge ya kusata ya yi kiwo a cikinsa, ku saurara! lallai kowane sarki yana da shinge, ku saurara! lallai shingen Allah shi ne abubuwan da ya haramta, ku saurara lallai! Lallai a jiki akwai wata tsoka, idan ta gyaru jiki ya gyaru dukkaninsa, idan ta ɓaci jiki ya ɓaci dukkaninsa, ku saurara! ita ce zuciya".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi

Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka ruwaito shi