Skip to content
839 Hadisai

Kundin Hadisan Annabi

Tace sakamako

9 daga cikin katuna 839

Cire tacewa
"Wanda ya yayewa wani mumini wani baƙin ciki daga baƙin cikin duniya Allah Zai yaye masa wani baƙin ciki daga baƙin cikin ranar alƙiyama, wanda ya yalwatawa wanda yake cikin matsuwa to Allah Zai yalwata masa a duniya da lahira, wanda ya suturta wani musulmi Allah Zai suturta shi a duniya da lahira, Allah Yana cikin taimakon bawa matuƙar bawan yana cikin taimakon ɗan'uwansa, wanda ya bi wata hanya yana neman Ilimi a cikinta to Allah Zai sawwaƙe masa hanyar shiga aljanna da ita, kuma wasu mutane basu taru ba a wani ɗaki daga cikin ɗakunan Allah suna karanta littafin Allah kuma suna dirasarsa a tsakaninsu sai nutsuwa ta saukar musu, kuma rahama ta lullubesu, mala'iku sun kewayesu, kuma Allah Ya ambacesu a cikin wadanda ke tare da shi, wanda aikinsa ya jinkirtar da shi to nasabarsa bazata gaggauto da shi ba".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
Wanda Allah yake nufin shi da alheri sai ya fahimtar da shi addini to, Ni dai mai rabawa ne, Allah ne Yake bayarwa, wannan al’ummar ba za ta gushe ba tana tsaye akan al’amarin Allah, wanda ya saɓa musu ba zai cutar da su ba, har al’amarin Allah ya zo.
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
"Lallai daga cikin alamomin tashin Alkiyama, za’a dauke ilimi, jahilci zai yi yawa, zina zata yawaita, za’a yawaita shan giya, maza za su yi karanci, mata za su yi yawa, har sai ya kasance mata hamsin mutum daya ne yake kula da su".
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi
Wadanda suka kasance suna karantar damu daga sahabban Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - sun zantar damu cewa su sun kasance suna koyan ayoyi goma daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ba sa koyan wasu goman daban har sai sun san abinda ke cikin wadannan na ilimi da aiki, suka ce: Sai muka koyi ilimi da aiki.
Hasan ne Ahmad ne ya rawaito shi
"Ya kai baban Munzir, shin ka san wacce aya ce daga littafin Allah mafi girma tare da kai?" ya ce: Na ce: Allah da Manzonsa ne mafi sani. Ya ce: "Yakai baban Al-Munzir, shin ka san wacce aya ce daga littafin Allah mafi girma tare dakai?" ya ce: Na ce; {Allah wanda babu wani abin bautawa da gaskiya sai Shi Rayayye Tabbatacce da kanSa} [Al-Baqara: 255]. Ya ce: Sai ya daki kirjina, ya ce: "Wallahi ilimi ya faranta maka kai baban Al-Munzir".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
Lallai cewa Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya fito ga wata halƙa daga sahabbansa, sai ya ce; "Me ya zaunar da ku?" suka ce: Mun zauna muna ambatan Allah muna gode masa akan abinda ya shiryar da mu na musulunci, kuma ya yi baiwa da shi garemu, ya ce: "Kun rantse da Allah babu abinda ya zaunar da ku sai hakan? suka ce: Wallahi babu abinda ya zaunar da mu sai hakan, ya ce: "Amma ni ban rantsar da ku ba dan tuhuma gareku, sai dai cewa (Mala'ika) Jibril ya zo min sai ya ba ni labarin cewa Allah - mai girma da ɗaukaka - Yana yi wa mala'iku alfahari da ku".
Ingantacce ne Muslim ne ya rawaito shi
"Allah Ya ni'imtar da mutumin da ya ji wani abu daga gurimmu sai ya isar da shi kamar yadda ya ji, da yawa wanda aka isarwa yana zama mafi kiyayewa daga wanda ya ji".
Ingantacce ne Tirmizi da Ibnu Majah da Ahmad Suka ruwaito shi
«Kwatankwacin abinda Allah Ya aikoni da shi, na shiriya da ilimi kamar kwatankwacin girgije ne mai yawa da ya zuba a wata ƙasa, daga cikinta akwai tsarkakakkiya, ta karɓi ruwa, sai ta tsirar da ciyawa mai yawa, kuma daga cikinta akwai mai fari, ta riƙe ruwan, sai Allah Ya amfani mutane da ita, sai suka sha suka shayar, kuma suka yi shuka, kuma ruwan ya samu wani ɓangare daban, wanda shi kawai faƙo ne ba ya riƙe ruwan kuma ba ya tsirar da ciyawa, to hakan kwatankwacin wanda ya fahimci Addinin Allah ne kuma Ya amfanar da shi da abinda Allah Ya aikoni da shi, sai ya sani ya kuma sanar, da kwatankwacin wanda bai ɗaga kai ba da hakan, kuma bai karɓi shiriyar Allah ba wacce aka aikoni da ita ba».
Ingantacce ne Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi