Skip to content

Ka ce: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, zan yi maka shaida da ita ranar Alkiyama

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - ya ce:

Manzon Allah - tsira da amincin Alah su tabbata agare shi - ya cewa Baffansa; "Ka ce: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, zan yi maka shaida da ita ranar Alkiyama", ya ce: Da badan Kuraishawa zasu aibatani ba, zasu ce: Razani da tsoron mutuwa ne suka kai shi haka ba da na faranta ranka da ita. Sai Allah Ya saukar: {Lallai kai ba zaka shiryar da wanda ka so ba saidai Allah Yana shiryar da wanda yake so} [Al-Kasas; 56].

قَالَ رَسُولُ اللهِ صَلَّى اللهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ لِعَمِّهِ: «قُلْ: لَا إِلَهَ إِلَّا اللهُ، أَشْهَدُ لَكَ بِهَا يَوْمَ الْقِيَامَةِ»، قَالَ: لَوْلَا أَنْ تُعَيِّرَنِي قُرَيْشٌ، يَقُولُونَ: إِنَّمَا حَمَلَهُ عَلَى ذَلِكَ الْجَزَعُ لَأَقْرَرْتُ بِهَا عَيْنَكَ. فَأَنْزَلَ اللهُ: {إِنَّكَ لا تَهْدِي مَنْ أَحْبَبْتَ وَلَكِنَّ اللهَ يَهْدِي مَنْ يَشَاءُ } [القصص: 56].

Muslim ne ya rawaito shi
Ingantacce ne
Bayani

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya nema daga baffansa Abu Dalib alhali shi yana magagin mutuwa da ya furta; Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, dan ya cece shi da ita ranar Alkiyama , kuma ya yi masa shaidar Musulunci, sai yaki furta shaidar dan tsoron kada Kuraishawa ta zargeshi ta ce da shi: Cewa shi ya musulunta ne saboda tsoron mutuwa da rauni! sai ya cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi: Da badan haka ba da na shigar da farin ciki a zuciyarka da furta shaidar, na isar da burinka har ka yarda! sai Allah Ya saukar da ayar da take nuni akan cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ba ya mallakar shiriya ta dacewa da Musulunci, kawai Allah - Mai girma da daukaka -Shi kadai ne Yake datar da wanda Yake so. Kuma Annabi - tsira da aminci su tabbata agare shi -yana shiryar da halitta ta shiryarwa da bayani da kira zuwa hanya madaidaiciya.

Ma"anonin Kalmomi

...:

Daga Cikin Fa idodin Hadisin

Ba'a barin gaskiya dan tsoro daga zancen mutane.

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - kadai yana mallakar shiriyar nuni ne da fadakarwa kawai ba shiriyar dacewa ba.

Halaccin ziyarar kafiri mara lafiya dan kiransa zuwa ga Musulunci.

Kwadayin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - akan kira zuwa ga Allah - Madaukakin sarki - a kowane hali.

Manazarta

Sahih Muslim (1/ 55) (25).

Kari (2)

البحر المحيط الثجاج في شرح صحيح الإمام مسلم بن الحجاج (1/ 539).

النهاية في غريب الحديث والأثر (ص 742).